Dalilan Da Suka Sa Na Bar Aikin Banki Na Koma Noma

Samuel Aende, dan kimanin shekaru 30, ya yi murabus daga aikin banki inda ya koma harkar noma gadan gadan.

Mista Aende wanda ya shafe sama da shekaru 10 yana aikin banki, ya jefa kudadensa a harkar noma harkar da ko kadan bai taba zama a aji a kansa ba.

Domin samun gamsuwa a harkar noma, Mista Aende ya shiga ya fara zuwa daukar bitar karatu akan harkar noma wanda hakan ya ba shi damar tattara bayanan da ake buƙata don bunƙasa a harkar noma.

Daga nan sai ya ziyarci kasar Isra’ila da Jamhuriyar Benin don neman ƙarin ilimi da ƙwarewa don gudanar da aikin gona yadda ya kamata.

A gonarsa mai suna Terjimin Farms Limited, mai fadin hekta 12 da ke garin Masaka karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa, a duk mako, yana samar da tan na tumaturi biyu da barkonon tsohuwa.

“Noman kayan lambu yana da matukar muhimmanci saboda yana samar da kayayyaki a koyaushe, musamman ma lokacin da ba noman su ba sosai. Wannan yana ba da damar samun kasuwa, wanda hakan riba ne ga manomi da ‘yan kasuwa,” in ji Mista Aende a wata hira da ya yi da Daily Trust.

Ya yi nuni da cewa noman kayan lambu na iya zama mai hadari kamar kowace irin sana’a, amma duk da haka, yana bukatar hakuri daga duk mai sha’awar sana’ar don samun nasara.

Mista Aende ya yi Allah wadai da yadda bankuna ke shakkar bai wa manoma bashi, yana mai cewa “A nan ne ya kamata a samar da tsare-tsare don tunkarar wannan tsari. Riban ya yi yawa shi ya sa karbar bashi yake wa manoma wahala.”

Ya kara da cewa, “Ban taba dana sanin abun da na yi ba ko na yanke, saboda wanan sana’a ya bude min ido sosai. Na samu damar koyawa mutane ilimi, tafiye-tafiye don tallafawa kananan sana’o’i da kungiyoyi masu zaman kansu ta hanyar fasaha tare da abubuwan da na samu. Ya ba ni bude ido a harkar noma da kasuwanci da rayuwa wanda da na zauna a harkar banki da ban samu ba, ba zan taba dainawa ba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories