‘Yan Daba Sun Hallaka ‘Yar Hidimar Kasa A Kaduna, Sun Wafce Mata Waya

Hukumar gudanarwar hukumar da ke kula da matasa masu yi wa kasar nan hidima (NYSC) ta yi juyayin mutuwar wata ‘yar hidimar kasa, Joel Grace Chalya KD/23A/4386, wacce aka kashe da safiyar ranar Laraba a Kaduna.

Rahotonni sun ce wasu ‘yan daba ne suka daba wa marigayiyar wuka tare da kwace mata waya a Barnawa GRA da ke Kaduna, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwarta.

Abokan marigayiyar sun yi gaggawar sanar da hukumar NYSC inda ita kuma hukumar ta yi gaggawar kaita zuwa asibitin Harmony da ke Barnawa a jihar Kaduna har ma ta fara farfadowa daga jinyarta amma daga bisani rai ya yi halinsa.

Hukumar NYSC ta cikin wata sanarwa dauke da sanya hannun Eddy Megwa, daraktan yada labarai na hukumar, ta nuna matukar damuwarta kan lamarin tare da mika jajenta da ta’aziyyarta ga iyalan mamaciyar, abokanta da kuma wurin da take aikin hidimta wa kasa.

Sanarwar ta ce, “Muna kan aikin hadin guiwa sosai da hukumomin tsaro domin tabbatar da an tsagulo da hukunta wadanda suka aikata wannan mummunar aikin na dabbaci domin tabbatar da wanzar da adalci.

“Muna kira ga jama’a da su yi aikin hadin guiawa da jami’an tsaro domin tabbatar da dukkanin masu hidimar kasar da aka tura yankunansu sun samu cikakken kariya domin bada tasu gudunmawa wajen cigaban kasa,” sanarwar ta shaida.

Ta kara da cewa, “Matasa masu yi wa kasa hidima ‘ya’yanmu ne, ‘yan uwanmu ne, kannenmu ne, dole ne mu hada kai da dukkanin ‘yan kasa mu karesu,” sanarwar ta bukata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories