‘Yan Fashin Daji Sun Kashe Limami Da Wani A Kaduna, Sun Jikkata 2

Da safiyar ranar Talata ne wasu ‘yan bindiga dadi suka kashe masu ibada mutum biyu a cikin wani masallaci da ke Sabon Layi a gundumar Kakangi da ke karamar hukumar Birnin-Gwari a jihar Kaduna tare da jikkata wasu karin biyu.

An nakalto cewa ‘yan ta’addan sun mamaye masallacin Ga Allah Babba da ke Sabon Layi tare da bude wuta ga masu sallar lamarin da ya janyo suka kashe limamin da wani mutum guda nan take.

Limamin masallacin, Malam Mamuda da wani Kabiru na unguwar Ga Allah Babba su ne aka kashe. Yayin da kuma Bilya Mairabo da Ashiru Mairabo suka gamu da munanan raunuka inda suke amsar kulawar likitoci a babban asibitin Jibrin Maigwari da ke Birnin-Gwari.

Shugaban wata kungiyar wandar da tsaro da shugabanci na kwarai a Birnin Gwari, Ibrahim Abubakar Nagwari, shi ne ya tabbatar da labarin harin, ya ce, kusan kullum ‘yan ta’adda na cin karensu babu babbaka a karamar hukumar Birnin-Gwari tare da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Ya kara da cewa lamarin ya yi kamari a kan hanyar Birnin-Gwari zuwa Kaduna da hanyar ta zama barazana ga matafiya a kowani lokaci.

Idan za a tuna dai a baya-bayan nan ‘yan bindigan sun kashe wani mafarauci, Bashir Unguwar Shekarau, da wasu direbobi biyu, Mustapha Adamu da Malam Muktar a kan babban hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Ba a samu ji ta bakin kakakin rundunar ‘yansandan jihar Kaduna, ASP Munsur Hassan ba dange da wannan lamarin har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories