Najeriya za ta sake karɓar $150m da Abacha ya ajiye a waje

A ranar juma’ar da ta gabata a Abuja Hukumomin kasar Faransa suka ayyana dawo da dala miliyan 150 wanda ake zargin marigayi tsohon shugaban kasa, Sani Abacha ya yi sama da fadi da su.

 Ministar kula da harkokin kasashen Turai da harkokin Faransa Catherine Colona ta shaidawa taron manema labarai cewa kasar Faransa za ta mayar da kudaden ne domin karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu.

 “Faransa za ta dawo wa Najeriya kadarorin da marigayi Abacha da iyalansa suka ajiye a kasar Faransa.

“Za mu fara tattaunawa da gwamnatin Najeriya domin ware wadannan kudade dan ayi ayyukan raya kasa da su wanda hakan zai amfani jama’a, bisa ga kudirorin da gwamnatin Najeriya ta sa gaba,” Catherine ta bayyana.

 Ta bayyana cewa sun dauki wannan alkawari ne sakamakon neman alfarma da ma’aikatar shari’ar Najeriya ta mika wa gwamnatin Faransa.

 Madam Colonna ta kara da cewa, domink karfafa alakar da ke tsakanin Najeriya da Faransa, Suna kokarin kara karfafa wannan alaka a shekarar da ta gabata da ma sauran shekaru masu zuwa.

 “Na yi matukar farin ciki da samun tarba daga wurin Shugaba Bola Tinubu.  Inda muka Tattauna kan yanayin kawancen kasashen biyu da kuma manyan rikice-rikicen yankuna da ma na duniya baki daya.

 “Na gode masa sosai saboda halartar taron koli kan sabuwar yarjejeniya hada-hadar kudade ta duniya da muka shirya a Paris a watan Yuni

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories