Bincike: Yadda Rashin Tsaftaccen Ruwa Ke Gurgunta Harƙar Ilimi A Matakin Farko

Daga Usman Babaji

Matsalar ƙarancin samun wadataccen ruwan amfanin yau da kullum a makarantu daban-daban da ke jihar Bauchi na barazana ga ɗaurewar harƙoƙin ilimi a matakin farko da kuma samar da ilimi mai inganci. Matsalar na gurgunta yunƙurin majalisar ɗinkin duniya kan shirin cimma muradin ƙarni wanda hukumar kula da ilimin a matakin farko ta ƙasa (UBEC) ke aiwatarwa. A wannan binciken da WikkiTimes ta gudanar, ta gano yadda ɗalibai ke rasa tsaftaccen ruwa wanda aka tilas suke neman ruwan amfani marar tsafta domin biyan buƙatun kansu wanda hakan kai tsaye na barazana ga kiwon lafiyarsu.

Ɗalibai a makarantun firamare da ƙaramin sakandari da suke sassan jihar na matuƙar fama da rashin samun ingataccen ruwa. Matsalar, ta na kai ga ga yaran (ɗalibai) su kasance na da zaɓi guda biyu ran, ko su sha ruwa marar tsafta ko kuma su koma gidajensu wanda mafi yawansu ba su iya zaɓan zuwan gidan domin shan ruwa da dawowa makaranta, yayin da wasu kuma in sun tafi neman ruwa mai kyau a gida ba su iya dawowa aji domin ɗaukan darasi. Matakin da bincikenmu ya gano na matuƙar gurgunta yunƙurin yaran na samu wadacacce kuma ingatacce ilimi.

Kazalika, halin da makarantun ke fuskanta, na sanya ɗalibai da malamai su dogara da amfani da hanyoyin ruwa marar tsafta da suke samu a kusa da su (Rafi), kuma, a wasu lokutan su na kamu da cututtuka sakamakon amfani da ruwa marar tsafta. Wannan batun ya kasance a zahirance a sama da makarantu guda takwas da WikkiTimes ta ziyarta.

Bayan gomannin shekaru da kafata, makaranta Firamare da ƙaramin sakandarin Nadabo da ke ƙaramar hukumar Tafawa Balewa, a jihar Bauchi har yanzu na fuskantar matsalar rashin ingantacce ruwa. Wannan matsalar ta jima tana ciwa malamai, ɗalibai, ma’aikata da al’umman yankin tuwo a kwarya.

Kusa da makarantar akwai wata rijiya da ke kusa aka gina domin yin alola. Wannan kuma ya kasance inda ake sa ran samun ruwa mai kyau. Amma, binciken da WikkiTimes ta gudanar, ta gano mata cewa rijiyar na fama da tsutsotsi. Don haka yara na shan ruwa marar tsafta da ka iya shafar kiwon lafiyarsu.

Don haka, iyaye da dama na fuskantar yadda yaransu ke kamu da ‘yan cututtuka da suke samowa sakamakon rashin ingantaccen ruwan da za su yi amfani da shi tun a makarantarsu.

“Bayan fama da cutar taifot (typhoid) da yara suka sha fama da shi, na gargaɗesu da su daina shan ruwa a makaranta gaba ɗaya,” Musa Isah, wani mahaifi da ke da ɗalibai uku ya shaida mana.

A wata makarantar ma, shugaban makarantar Firamare ta Tashan Durmi da ke ƙaramar hukumar Toro, Alhassan Mohammed Abubakar, ya ma kasa danne damuwarsa, ya ce, baya ga cututtuka da ake kamuwa da su sakamakon rashin ruwa mai tsafta, ƙarancin ruwan na janyo hana yara zuwa makaranta.

“Rashin wadataccen ruwan amfani na hana wasu ɗaliban zuwa aji domin ɗaukan darasi,” ya shaida.

A ƙasar Najeriya, haƙƙin yara ne samun ilimi a matakin farko domin su samu damar kyautata rayuwarsu ta gaba. Sashi na 15 na dokar kare ‘yancin yara na cewa, kowani yaro na da haƙƙin samun ilimi kyauta kuma dole ne a ba shi ilimi a matakin farko, kazalika, haƙƙin ne na gwamnati ta samar da wannan damar ga kowani yaro.”

Sai dai kuma, ba kowani yaro ne a Najeriya zuwa makaranta ba, musamman a arewacin Najeriya. Hakan na haifar da rashin ilimi da janyo yaran da basu zuwa makaranta.

Asusun kula da yara na majalisar ɗinkin dinkin duniya (UNICEF) ya nuna cewa samar da wadatacce kuma ingantaccen ruwan amfani na taimakawa wajen bai wa yara zarafin zuwa makaranta da kula da kiwon lafiyarsu da zai taimakesu cimma muradinsu na rayuwa.

ƘALUBALEN RASHIN RUWA MAI INGANCI A MAKARANTU

Sarkin Nadabo, Abdullahi Ya’u, a matsayinsa na shugaban al’umma, ya yi iyaka ƙoƙarinsa wajen ganin an samu cigaba ƙauyensa amma abun ya citura.

Abun takaici, makarantar Firamare da ƙaramin sakandarin Nadabo ne kawai makarantu a yanki. Ya ce, sun shafe tsawon shekaru su na fama da matsalar ruwa amma har yanzu jiya-i-yau, “Matsalar ruwa na hanamu barci,” ya shaida wa WikkiTimes.

Ya’u ya nuna mana hujjojin ayyukan da aka yi watsi da su da ka iya zama mafita ga matsalar ruwa da ake da shi a yankin. Ya jagoranci wakilinmu zuwa wata fanfon tuƙa-tuƙa da ƙarfinka, wanda aka gina amma har yanzu tun bayan shekara goma ba a kammala ƙarasata ba balle jama’a su mora. Kawai fanfon tuƙa-tuƙar ya kasance yashe ba tare da ana cin gajiyarsa ba.

“Ba a kammala ginawa ba balle ma a taɓa amfani da shi, don haka bai taɓa amfani ba,” ya bayyana.

Ɗalibai makarantar na amfani da wata rijiyar da aka gina domin yin alwala a matsayin hanyar samun ruwan amfani a garesu. Duk kuwa da cewa ruwan na yankewa a lokacin rani, kodayake, al’ummar sun yi amannar ruwan bai da ingancin da za a iya sha.

Ya’u ya yi bayanin cewa, duk da sauran matsalolin da makarantar ke fuskanta, ƙarancin ruwan sha na hana yara da dama samun kwanciyar hankalin koyon ilimi.

Musa Isah mazaunin ƙauyen kuma na da ‘ya’ya uku ɗalibai. Ya yaransu sun sha fama da cutar taifot sakamakon ruwa marar kyau da suke shawowa idan sun je makaranta domin ba su da wadataccen ruwan samun ruwa a makaranta

Isah ya nuna cewa, a lokacin rani an fi fuskantar matsalar ruwan amfani a makarantar wanda hakan ke zama damuwa sosai a garesu.

“Yana zama musu abun wuya su samu ruwan da za su wanke hannunsu bayan sun yi Kashi (sun zaga bayan gida), wanda da wannan hannun ne suke amfani wajen cin abinci, wannan wani matakin ne da ke ƙara jefa kiwon lafiyar ɗaliban cikin haɗari,” ya ƙara da cewa.

Kazalika, sauran makarantun ma suna fuskantar irin wannan matsalar da suka haɗa da firamaren Tashan Durumi da ke gundumar Jama’a a ƙaramar hukumar Toro, wacce ke da ɗalibai sama da 1,000 a cewar mamban kwamitin kula da makaranta (SBMC) Bashir Mohammed.

Ya ce, tun lokacin da wurin samun ruwa na wucin gadi da ya lalace na makarantar tsawon shekaru, suna yin tattaki zuwa wuri mai nisa domin neman ruwan.

A cewarsa, a wasu lokutan, a ƙoƙarin ɗaliban na samun ruwa suna rasa aji ba su samun darussan da ake koyar musu, inda ya ce, hakan na sanya su yi watsi da koyon karatu domin neman ruwan amfani.

Malami a makarantar, Alhassan Mohammad Abubakar, ya shaida ma WikkiTimes cewa, babban matsalar da makarantar ke fuskanta a halin yanzu sun haɗa da rashin ruwa, rashin bayan gida, gine-gine da kuma kujerun karatu.

Abubakar ya bayyana cewar sun sha ruwata ƙorafinsu ga hukumomin da abun ya dace amma babu sakamakon da suke samu. Kan hakan, ya yi bayanin yadda ɗalibai ke sanya rayukansu cikin hatsari wajen tsallaka babban hanyar Bauchi zuwa Jos domin neman ruwa, kuma wasu in sun tafi neman ruwa ba su dawowa makaranta.

“Idan da muna da ruwa a cikin makarantar, ba za a samu irin wannan matsalar na firgici da damuwa da muke ciki kullum ba, domin yaran nan na sanya rayuwarsu cikin hatsari na tsallaka titi domin babban hanya ce da direbobi ke gudu sosai,” ya shaida.

Hakan wannan matsalar take a lokacin da WikkiTimes ta ziyarci Firamaren Kutaru (Kwanar Dutse) da ke cikin kwaryar Bauchi, inda shugaban makaranar Abubakar Usman, a wasu lokutan daliban makarantar na zuwa rafi domin neman ruwan sha.

Ya nuna damuwarsa kan cewa a bisa watsi da makarantar da hukumomi suka yi, ya sanya ɗalibai da dama suke rasa kwarin guiwar zuwa azuzuwa domin ɗaukan darasi, “Ba su zuwa makaranta a kai a kai, ka kalli makarantar nan babu wani abun da ke aiki a ciki.”

Wakilinmu ya naƙalto cewa ɗalibai 50 ne kawai ya ci karo da su a makarantar lokacin da ya kai zirarar.

Kusan kilomita biyar daga makarantar firamare ta makiyaya inda makarantun guda biyu suke kan hanyar Mararaban Liman Katagum. Babban makarantar firamare ta Maraba, mai ɗalibai 640, ba su da wurin samun ruwa na tuƙa-tuƙa, yayin da makarantar makiyayan da ke da dalibai 1,000 amma ba su da wurin samun ruwa.

Makarantar makiyaya ta Fikaji da  Dapasu, da kuma Polchi duka da suke ƙaramar hukumar Tafawa Balewa da firamaren Kanwaya da ke ƙaramar hukumar Toro, dukka suna amfani da rafi a matsayin hanyar samun ruwa, kuma ana fuskantar matsalar rashin ruwa a cikin makarantun.

Abdulsalam Abubakar, mazaunin Kanwaya, ya ce, firamaren Kanwaya na fama da matsalar ruwan amfani duk da ɗalibai sama da ɗari uku da suke karatu a ciki kuma akwai matsalar ban-ɗaki ma.

Bello Musa, malami a makarantar makiyaya ‘Fikaji Nomadic’, ya tabbatar da cewa ɗalibai na amfani da rafi domin neman ruwan sha. Ya buƙaci masu mallakin makarantar da su gaggauta samar da rijiya ko fanfon tuƙa-tuƙa a makarantar, “Kuma muna son a yi kwaskwarima ga makarantar,” ya shaida.

Musa ya ce makarantar na fama da lalacewar azuzuwa. A cewarsa, ɗalibai sama da 220 ba su da ajin karatu da zai karesu daga ruwan sama a lokacin damina, ya ƙara da cewa waɗannan matsalolin na shan harƙoƙin karatunsu.

Majiyoyi daban-daban sun tabbatar mana cewa makarantu daban-daban a sassan ƙananan hukumomi 20 na jihar Bauchi na fama da irin wannan matsalar na rashin ingataccen ruwa a makarantu, lamarin da ke barazana ga harƙoƙin ilimin yara.

Bayanan da ke ƙara na nuni da cewa jihar Bauchi na daga cikin jihohin da ke gaba-gaba wajen fama da yara da basu zuwa makaranta a jihohi 19 da suke arewacin Nijeriya, da yara sama da miliyan 1.2 ba su halarci makaranta ba tun a makatakin farko.

Har ila yau, ƙungiyoyin fararen hula da dama (CSOs) da ‘yan rajin kare haƙƙin bil-adama sun yi ta suka kan karancin ruwa a makarantu a cewar Hummanium, ƙungiyar farar hula ta ƙasa da ƙasa, na cewa, muddin yara suka yi mu’amala da ruwa marar kyau, ka iya janyo cutuka ga ɗalibai da ka iya rabasu da makarantu.

ƁARKEWAR AMAI DA GUDAWA A MAKARANTU

Kamar makarantar Nadabo, inda cutuka irin su Taifot suka kasance babban abun da ke damun iyaye, ita ma makarantar Luri da ke Tafawa Balewa da da babban firamaren Mararaba ta taɓa fuskantar ɓarkewar cutar Kwalara. Yayin da ita ma makarantar Luri ta taɓa samun kanta a hakan.

Shugaban makarantar Luri, Ja’afaru Adamu, ya ce, a shekarar 2021, makarantar ta fuskanci ɓarkewar cutar Kwalara a tsakanin wasu ɗalibai lamarin da ya sanya makarantar ta dakatar da harƙoƙin karatu na tsawon wata guda.

Adamu ya misalta rashin ingataccen ruwa da bayan gida a makarantar a matsayin dalilin da ya janyo ɓarkewar cutar.

A makarantar firamare na Mararaba, ɗalibai da dama ne aka bada labarin sun taɓa kamu da cutar Kwalara,” wasu ɗaliban sun kamu da cutar kwarala,” a cewar shugaban makarantar Adamu Garba.

Garba ya misalta cutar mai mummunar haɗari a matsayin rashin hanyar ruwan sha da kuma rashin ban-ɗaki a makarantar.

GWAMNATI TA TOFA ALBARKACIN BAKINTA

Jami’in watsa labarai na hukumar kula da ilimi a matakin farko ta jihar Bauchi (SUBEB), Mohammed Abdullahi, ya ce, an samu wannan matsalar ne sakamakon ƙaruwar yawan makarantu a faɗin jihar. Ya ce, duk da gwamnati ta taka muhimman rawa ta hannun hukumar samar da ruwa a yankunan karkara ta jihar (RUWASSA), da ƙungiyoyin daban-daban suka bayar da nasu gudunmawar a ɓangaren harƙoƙin ruwa, “Muna da ƙungiyoyin daban-daban da suke taimaka mana wajen samar da ruwa.”

Ya ce, makarantun ne suka yi matuƙar yawa, amma gwamnati tana iyaka bakin ƙoƙarinta wajen wadata makarantu da ruwan amfani a kowani lokaci.

Abdullahi ya yi bayanin cewar hukumarsu tana da makarantu sama da 3,000 da suke ƙarƙashinta a sassan jihar, don haka za a iya samun wasu ƙalilan da suke fuskantar matsalar ƙarancin ruwa.

Ya ƙara da cewa yadda yara ke shigowa jihar Bauchi daga jihohin makwafta sakamakon rikicin ta’addanci, hakan na daga cikin dalilan da suke ƙara shafan makarantu da janyo matsaloli ga tsare-tsaren kula da makarantu.

Sannan, ya nuna cewa, akwai matsalar rashin sanya ido da kulawa ga kayayyakin da gwamnatin ta samar a makarantu daga wajen jama’an yankunan.

Ya tabbatar da cewa gwamnati ta na da burin shawo kan dukkanin matsalolin da suke fuskantar yara a makarantu, inda ya ce, nan kusa matsaloli da dama za su zama tarihi domin kyautata ɓangaren koyo da koyarwa.

Duk ƙoƙarin da WikkiTimes ta yi domin jin ta bakin hukumar RUWASSA kan waɗannan matsalolin, haka ba ta cimma ruwa ba domin masu alhakin amsa tambayar sun gagara cewa komai kan buƙatar da aka shigar musu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories