Bayan Shekaru 62 Masarautar Ningi Ta Nada Sabon Waziri

A karon farko bayan shekaru 62 da masarautar Ningi ta dakatar da Sarautar waziri, Sarki Dr Yunusa Muhammad Danyaya ya nada Ambasada Shuaibu Adamu a matsayin sabon Wazirin-Ningi na hudu.

WikkiTimes ta ruwaito cewa Masarautar Ningi ba ta da Waziri tun a shekarar 1961 lokacin da gwamnatin yankin Arewa ta bayar da umarnin a dakatar da ofishin domin wanzar da zaman lafiya a Masarautar.

Sarkin ya bayyana cewa ya dace kuma ya kamata a ce an cike gibin sarautar Wazirn masarautar don haka ne Majalisar zartaswa na Masarautar ta yanke shawarar nada shu’aibu Adamu.

“Zaben da aka yi ba abu ba ne da ya kasance mai sauki sakamako da kuma nadin Amb. Adamu a matsayin Wazirin Ningi.

“An zabo Adamu ne bisa la’akari da tarihinsa, yi wa al’umma hidima, kyawawan halaye da kuma goyon bayan sa ga Sarki da Masarautar.

“Sarautar Waziri sarauta ce mai girma da tasiri sosai a harkokin mulkin masarautar,” cewar sarkin.

Sarkin ya bayyana cewa Waziri shi ne shugaban sarakuna na masarautar.

A nasa bangaren, sabon wazirin Ningi Ambasada Shuaibu Ahmed Adamu yi alkawarin yin biyayya ga masarautun da kuma ita kanta majalisar masarautar.

Ya kuma tabbatar wa al’ummar Masarautar cewa zai yi amfani da karfin kujerarar sa wajen kai masarautar gaba.

WikkiTimes ta tattaro cewa Ambasada Adamu ya kasance tsohon jakadan Najeriya ne a kasar Qatar tun zamanin gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan kuma ya taba rike kujerar mai bai wa tsohon gwamnan jihar Bauchi Ahmed Adamu Muazu shawara na musamman.  

A halin yanzu, kuma shi ne Babban Sakatare kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Majalisar tattara bayanai ta Kudi na Gwamnatin Tarayyar Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories