Safarar Mutane:’Yan sanda sun yi nasarar ceto Mutane 60 a Jigawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da safarar mutane tare da tilasta musu aikin wahala.

 Rundunar ‘yan sandan ta ce wadanda ake zargin na daga cikin mambobin kungiyoyin da suka kware wajen safarar mutane zuwa yankin kudancin kasar nan da sunan neman kudi.

 Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa, Lawan Shi’isu Adam, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, ya ce an kama wadanda ake zargin ne sakamakon  rahoto da suka samu daga Hakimin Marken Biki bayan sun tattare mutane kusan sittin da niyar tafiya da su jihar Osun.

 A cewarsa, tawagar jami’an ‘yan sanda daga sashin Babura karkashin jagorancin DPO sun yi nasarar isa kauyen inda suka cafke wasu mutane biyu da ake zargin da hannun su a wannan laifi.

 “A ranar 02/11/2023 Hakimin Marke Biki ya kaiwa ‘yan sandan Babura rahoton cewa wasu masu safara mutane sun dira garin Babura, in da suka dauki kimanin mutane sittin (60) da nufin tafiya da su zuwa jihar Osun domin yin aikatau”.

 “Bayan samun rahoton, jami’in ‘yan sanda na yankin nan take ya jagoranci tawagar ‘yan sandan zuwa kauyen inda suka chafke wani Omotosho Daniel mai shekaru 40 da haihuwa dan asalin karamar hukumar Ife ta Kudu a Jihar Osun, da Tanimu Usman mai shekaru 20 dan kauyen Kwadage da ke garin Roni Jihar Jigawa”, in ji shi.

 Adam ya kara da cewa a yayin gudanar da bincike, wadanda ake zargin sun amsa cewa suna daukar mutane zuwa yin aikin noma a jihar Osun, ba tare da neman izinin masu ruwa da tsaki ba.

 Kakakin ya kara da cewa ana gama bincike za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories