Me yasa halittar Mata ke sauyawa bayan aure?

Kamar yadda aka sani cewa kowace mace da irin kirar halittar da Ubangiji ya yi mata, amma tambayar anan ita ce me ya sa mata ke murjewa su yi ƙiba bayan sun yi aure.

Wannan lamari ba baƙo ba ne ga dukkan al’ummar ƙasar Hausa. In muka duba za mu ga cewa da yawa daga cikin matan Nijeriya musammam yankin Arewa da zarar mace tayi aure ba jimawa sai kaga halittar jikinta ya fara sauyawa ta yi ƙiba ta murmure duk tayani muni sun ɓace.

A al’adance al’ummar ƙasar hausa suna kallon wannan lamari a matsayin cigaba ga mace saboda ana ganin cewar tana samin matuƙar kulawa a wurin mijinta.

Amma sai dai tambayar anan ita ce kulawar miji ita ce babbar lamarin da ke sa jikin mace ya canza ko kuwa akwai wasu abubuwa?

Tabbas kulawar miji na janyo sauyi ga halittar mace amma hakan bai isa dalili ɗaya da za a ce shi ne ke janyo wannan sauyi ba.

Ga kaɗan daga cikin dalilan da ke sa mace samun sauyin halitta a gidan miji

Samun kwanciyar hankali

A lokacin da mace tayi aure za a ga cewa akwai wani kwanciyar hankali na musamman da zata fuskanta wanda duk inda ta je baza ta same shi ba sai a gidan miji ire-iren wannan sauyi sun haɗa da amarci, soyayya sannan kuma cima mai kyau, waɗannan abubuwa suna matuƙar tasiri a canjin halittar mace, cikin ƙanƙanin lokaci za a ga mace ta murmure ta murje.

Sabuwar Rayuwa da kuma samun ƴancin kai

Bayan soyayya a aure akwai kuma wasu tarin nauyi da zai hau kan mace wanda hakan kansa ta fahimce cewar girma da kulawar wasu mutane ya hau kanta kamar su rainon ciki, haihuwa da kuma renon Yaron da zata haifa.

Wannan sauyin da kwanciyar hankali suma suna kara taimakawa mace wajen zama babbar mata. Sai a ga cikin ƙanƙanin lokaci mace ta murje ta yi jiki duk wasu jijiyoyi, ƙasusuwa,da kuma kwayar halittunta sun sami sauyi sun buɗe wanda hakan zai sa alamar kiba ta bayyana.

Rainon Ciki

Bayan hidimar aure akwai babbar hidima a gaban ma’aurata wannan hidima itace ɗaukar ciki. Haihuwar Ɗa abu ne mai matukar daɗi da sa farin ciki kuma yana daga cikin abubuwa mafi sauƙi da ke ƙara wa mata buɗewar jiki ka ga sun yi ƙiba.

Daga lokacin da mace ta sami ciki to tabbas cin abincinta zai karu fiye da na da, za a ga idan a da ba cin ƙaramin kwano to daga ta sami ciki sai kaga abin ya canza, dole a nemo babban mazubi.

Mata yayin da suke da ciki suna matuƙar yin ciye-ciye sosai musamman abubuwa masu maiko wanda hakan ke sa jikin mace ya buɗe har ta yi jiki ta murmure.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories