Yadda Matashi A Bauchi Ya Yi Bikin Canza Wa ‘Yarsa Suna Zuwa Mahaifiyar Tinubu Don Murna

Domin nuna murna da nasarar da shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya samu a kotun koli, wani matashi a jihar Bauchi, Khamees Musa Darazo ya canza wa ɗiyarsa mai shekara biyu ‘Hauwa’ suna zuwa na mahaifiyar Tinubu, wato Abibatu.

Da ya ke magana yayin bikin addu’ar canza suna da walima da ya gudana a ‘Double 4 Event Center’, Bauchi, Khamees Musa Darazo, ya ce, wannan matakin, cika alƙawarin da ya ɗauka ne a kwanakin baya da ya ce muddin Tinubu ya samu nasara a kotun koli kan ‘yan adawarsa, to tabbas zai canza sunar ‘yarsa zuwa namahaifiyar shugaban ƙasa domin nuna murnarsa da farin cikinsa.

“Cike nake da farin ciki da a yau na canza wa ‘yata suna daga Hauwa zuwa Abibatu, mahaifiyar shugaban ƙasa Bola Tinubu, hakan wani mataki ne na ƙarfafa masa guiwa da nuna tsantsan soyayya a gareshi domin ya ci gaba da gudanar da kyawawan ayyukan da ya fara a ƙasar nan.”

“Ni masoyin Tinubu ne na haƙiƙa, idan za ku tuna a lokacin yaƙin neman zaɓe, lokacin ina matakin ɗan yi wa ƙasa hidima, na sadaukar da alawus xina ga Tinubu domin mara masa baya ga yunƙurin neman takararsa a 2023.

“Na yi hakan ne domin kwarin guiwar da nake da shi na cewa Tinubu ya zo da alkairan da zai iya shawo kan matsalolin da Nijeriya ke ciki, kuma ina da yaƙinin in aka ba shi dama kwalliya za ta biya kuɗin sabulu, a hakan ne muka dafa masa baya muka shiga gangamin wayar da kan jama’a a tsakanin jihohin Bauchi da Gombe domin nema masa ƙuri’u.

“Cikin yardar Allah aka samu nasara. Don haka ne na ce idan Allah ya tabbatar da nasararsa a kotun koli zan canza wa ɗiyata suna, kuma Allah ya amsa da addu’armu, don haka a yau cika alƙawarin da na ɗauka ne.”

Ya shawarci al’ummar Nijeriya da su kasance masu haƙuri da juriya lura da yadda Tinubun ya amshi ƙasar nan, yana mai cewa yana da cikakken kwarin guiwar Tinubu na da basira da dabarun da kowani ɗan ƙasa zai yi alfahari da shi wajen kyautata shugabanci na kwarai.

Ya kuma yi amfani da damar wajen shawartar shugaban kasa Tinubu da ya yi aiki tuƙuru domin shawo kan matsalolin da ƙasar nan ke fuskanta ta yadda jama’a za su gamsu da irin kwarin guiwarsu a kansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories