Kotu Ta Sake Mayar Da Emefiele Gidan Yari Kan Rashin Cika Ƙa’idojin Beli 

Daga Halima Lukman 

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ta ɗage shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele zuwa watan Janairun 2024.

Hakan zai sa ya ci gaba da zama a gidan yarin Kuje da ke Abuja har sai ya cika ƙa’idar belinsa ta kudi naira miliyan 300.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ce, ta gurfanar da Emefiele bisa zarginsa da laifuka guda shida, ciki har da zargin badaƙalar kuɗi Naira biliyan 1.6 da kuma mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba.

Sai dai tsohon gwamnan babban bankin ya musanta zargin.

Yanzu kotun ta ayyana 18 ga watan Janairun 2024 domin cigaba da zama kan shari’ar.

Shugaba Bola Tinubu ne, ya dakatar da Emefiele daga muƙaminsa a ranar 9 ga watan Yuli 2023, don gudanar da bincike kan yadda ya tafiyar da ayyukan ofishinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories