Da Ɗumi-Ɗumi: ‘Yan Majalisan Dokokin Bauchi Sun Zaɓi Sabbin Shugabanni

‘Yan majalisun dokokin jihar Bauchi sun zaɓi Hon. Babayo Muhammad Akuyam, mamba da ke wakiltar mazaɓar Hardawa a matsayin sabon kakakin majalisa da zai cigaba da jagorantar harkokin majalisar.

Kazalika sun kuma zaɓi Hon. Ahmed Abdullahi da ke wakiltar mazaɓar Dass a matsayin mataimakin kakakin majalisar jihar.

A yayin zaman majalisar na ranar Laraba, mambobin sun cimma wannan matsayar ne biyo bayan da kotun ɗaukaka ƙara ta jingine nasarar tsohon kakakin Abubakar Y Sulaiman da mataimakinsa Jamilu Dahiru da suka samu tare da umartar a sake gudanar da zaɓe a wasu rumfunan mazaɓunsu.

Zaɓen na zuwa ne biyo bayan ƙudurin da ɗan majalisa mai wakilar mazaɓar Shira, Auwal Hassan ya gabatar yayin da ya samu marawar baya daga mamba mai wakiltar Burra, Tanko Ibrahim.

Dukkanin shugaba da mataimakin, akawun majalisar dokokin jihar, Umar Yusuf Gital ne ya rantsar da su.

A jawabinsa na ƙarɓar mulki, sabon kakakin, Babayo Akuyam ya sha alwashin kyautata shugabanci da yin aiki tare da kowa daga cikin mambobin majalisar.

Ya gode wa mambobin majalisar bisa kwarin guiwar su a kansa, inda ya yi alƙawarin yin jagoranci na kwarai.

Kazalika, gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad, zai gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2924 a gobe Alhamis.

Wannan bayanin na ƙunshe ne cikin wasiƙar da gwamnan jihar Bala Muhammad ya aike da shi majalisar mai ɗauke da sanya hannun sakataren gwamnatin jihar Ibrahim Mohammed Kashim wanda shugaban masu rinjaye a majalisar Sale Hodi Jibir ya karanto a yayin zaman majisar na ranar Laraba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories