DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnan Ondo Akeredolu Ya Rasu

Gwamnan Jihar Ondo, Arakunrin Rotimi Akeredolu, ya rasu.

Akeredolu, wanda shehin Lauya ne (SAN), an zaɓe a matsayin gwamnan jihar Ondo karo na farko a 2016.

Ya sha fama da jinya na tsawon lokaci inda a ‘yan watannin baya jikin nasa ya yi ƙamari, duk da cewa wasu sun yi ta kiran sa da ya yi murabus sakamakon tsananta da jikinsa ya yi amma hakan bai sa ya yi ba. 

Ya mutu ne da sanyin safiyar ranar Laraba.

A kwanakin baya gwamnan ya sake komawa zuwa ƙasar Jamani domin jinya inda ya miƙa ragamar mulkin jihar ga mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa, domin ya ci gaba da tafiyar da harkokin jihar a matsayin gwamnan rikon kwarya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories