NNPC Ta Ƙaryata Raɗe-Raɗin Ƙarin Farashin Mai

Hukumar gudanarwa na kamfanin Mai NNPC ta fito ƙaryata batun cewar farashin mai zai yi tashin Gwauron zsbiy.

 Sanarwar ta fito ne daga bakin Babban jami’in sadarwa na Kamfanin Olufemi O.Somaye a jiya Laraba 3 ga watan Janairu 2024 Inda yake cewa ”Hukumar gudanarwa na Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC) ta ƙaryata zancen da ke yawo na cewar kamfanin ta yi ƙarin farashin man fetur.”

 Kamfanin na NNPC ya buƙaci yan Najeriya da su yi watsi da duk wata jita-jita da ba su da tushe balle makama kuma sun ba da tabbacin babu wani shiri na sake ƙara farashin Mai.

 Haka kuma kamfanin ya shawarci masu ababen hawa da su daina fargaba saboda a halin yanzu akwai wadataccen Mai a ko ina a faɗin ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories