Ɗan Siyasar Da Na Bashi Goyon Baya Da Addu’o’i Shi Ya Min Cune Da DSS – Cewar Malam idris Dutsen Tanshi

A wata hira da DW Hausa ta yi da sanannen malamin addinini musulunci Sheikh Idris Dutsen Tanshi ,ya bayyana abubuwa biyar da ba zai taɓa manta su ba a rayuwarsa.

Malamin ya bayyana Abu na farko da bazai taɓa iya mantawa ba shine mutuwar mahaifinsa wato Malam Abdulaziz.

”Mahaifina Allah ya masa rasuwa ina yaro a lokacin sun rabu da mahaifiya ta ina yaro,har ya kasance shi ke kula da ni sai farat ɗaya Allah ya masa rasuwa.

Sai Abu na biyu malamin yace wani abun farin ciki ne ya same sa,yace wata rana misalin ƙarfe 12 na dare wani Bawan Allah ana ce masa Salihu yazo ya bugawa malam ƙofa ya yi masa albashir da an ɗauke sa a jami’ar Madina.

”Abu na uku shine wanda yake bani mamaki ga ɗan uwa mutum musulmi ,sai kaga mutum musulmi ya yadda cewar shi musulmi ne amma wai sai ace masa kar yayi koyi da kowa sai da Annabi,wannan Manzo da aka Turi masa.Amms sai kaga mutum na tawaye yana koyi da waɗan su mutane da ba a aiko su ba.Har mutun ya dinga tada jijiyar wuya akai,wannan abu na matukar bani mamaki.

Malamin ya ccigaba da cewa abu na hudu da ke bashi mamaki shine yadda ƴan siyasa ke mu’amala da malamai abun na matuƙar bashi mamaki.Yace yayi mu’amala da ƴan siyasa duba da zamanin da ake ciki ƴan siyasa na biyar malamai dan neman addu’a.”Amma daga lokacin da ka yi musu addu’a ka basu goyon bayan ka to suna samun kujerar da suke nema to kai ne zaka zama abokin hamayyar su.

”Akwai ɗan siyasar da yazo wurina ya nemi addu’a da shawarwari kuma ya nemi goyon bayan ɗalibai na kuma na yi masa iya ƙoƙarin a don cimma burin sa,amma abin mamaki sanadin sa DSS suka kamani aka Kani kurkuku na yi sati ɗaya a watan Ramadan.Aka hanani yaɗuwa da iyalaina aka hanani karatunsa duk saboda shi.”

Malamin Ya bayyana abubuwan da bazai manta ba in da ya zayyano Na biyar ya ke cewa mutun ya san cewa zai mutu amma kuma baya shirya mutuwa.Kullum ana mutuwa amma sai kaga mutum baya sa abin a lissafin sa.Malamik yace har zakaga mutane idan wani ya mutu sai kaji suna cewa ”Ahh yau wane an tafi lahira”.Saboda a rayuwar mutun gaba ɗaya bai tanadi mutuwar ba.Duniya Kawai suka sa gab

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories