Yadda Malamin Tsubbu Hassan Patigi Ke Azabtar Da Masu Jinya, Yi Wa Mutane Tsirara Tare Da Amshe Musu Kuɗaɗe

Sama da shekaru, Malam Hassan Patigi, daga yankin Patigi a jihar Kwara ya kasance na rangadi a garuruwa da ƙauyuka da dama a Najeriya da manufarsa na yunƙurin warkar da marasa lafiya da cetosu mutane daga ƙaƙaniƙayin damuwowi da rashin lafiyar da ya musu katutu. Sai dai, a ƙoƙarinsa na kai wa ga cimma hakan, lamarin na juyawa zuwa cin zarafin mutane, musamman a ƙauyukan jihohin Neja da Kwara. A lokacin da yake gudanar da ayyukansa, ana zarginsa da cewa, yana bayar da umarnin musgunawa da azaftar da maza, yayin da kuma wulaƙanta mata a bainar jama’a, da zarginsu da cewa su Mayu ne (Maita). Baya ga waɗannan haramtattun ayyukan nasa, ana kuma zarginsa da cewa yana amsar kuɗaɗe daga hannun waɗanda abun ya shafa, haifar da ɓaraka da kokonto a tsakanin iyalan waɗanda suka shiga hannunsa da wannan tunanin. A wani binciken kwakwaf da Yunusa Umar na WikkiTimes ya gudanar, ya bankaɗo yadda mutumin da ke kiran kansa da cewa ‘Bawan Allah’ a Najeriya, ke tauye wa al’umman ƙasa haƙƙinsu ba tare da ɗaukan wani mataki ko hukunci daga hukumomin ƙasar ba. Idris Khalid ne ya fassara.


Hassan Patigi, wani malamin Tsubbu ne da ke iƙirarin warkar da masu jinya ta farfaɗiyanci inda yake shirya gangamin aiki a bainar jama’a domin nuna musu irin salon aikinsa a yankuna daban-daban da ƙauyuka da ke shiyyar arewa ta tsakiya inda ke gayyatar mutane masu lalurar farfaɗiyanci da neman kuɗaɗe. Patigi ya kasance ya na yin addu’o’i a cikin sacet ɗin ruwa tare da umartar masu masa hidima da suke raba wa dandazon mutane sacet ɗin ruwan da ya ke iƙirarin ya musu addu’o’i ta baiwa a ciki da nufin taimakawa mutanen da suke da fama da cutuka daban-daban musamman waɗanda suka shafi na farfaɗiyanci da dangogin cutukan da maita ko aljanu ke janyo wa mutane.

Jerin mutanen da ake yawan kawo wa Patigi a yayin da ke baje basirarsa sun haɗa da makafi, kurame, guragu da kuma matan da ke neman haihuwa ko a ce mahaifa. ‘Yan mintuna bayan mutane sun sha ruwan, sai a ga wasu mutane sun fito da iƙirarin waraka daga cutuka duk da wasu mutanen ba su iya ganinsu ko gane su. Wani lokacin yana nuna kamar wani umarni yake samu daga wata duniyar ta daban wacce mutane ba ma su gane ta ina yake samun bayanansa, ko ya ce an umarceshi da ya yi kaza ko kaza.

Mutanen Da Dama Da Suka Ziyarceshi Masu Fama Da Cutuka Na Musamman Ba Su Warke Ba

Audu Suleiman, mazaunin ƙaramar hukumar Mokwa da ke jihar Neja, yana ɗaya daga cikin mutanen da suka je wurin Malam Patigi domin neman taimakonsa kan jinyar da ke damunsu. Yana fama da lalurar shanyewar ƙafafu tun shekarar 2016 kuma an danganta hakan da Maita. Don haka, ya ziyarci cibiyar warkarwar Patigi domin neman lafiya, amma duk da bayan kai ziyara da shan ruwan nasa na tsawon lokaci kuma sau tarin yawa, har yanzu bai samu lafiya ba.

“Na ziyarci cibiyoyin warkar da marasa lafiyarsa har sau uku, amma har yanzu ban samu lafiya ba. Yana faɗawa mutanen da suke fama da shanyewar ƙafafu da su tashi su tsaya, amma har yanzu ni kam ban samu sauƙi ba, ƙafafuna suna nan a shanye,” ya shaida wa WikkiTimes.

A dandamalin gudanar da aikin nasa, malamin tsubbun yakan miƙa yatsarsa kan mutanen da suke neman taimako a cibiyarsa ta mu’ujizzanci, da iƙirarin farauton Mayu (Maita) a jikin mutane a yunƙurinsa na kashe maitar da sauran mutane a yayin da ke baje baiwar tasa a taron jama’a da yake tarawa. Nna’ba, wata mace ce daga Bukka, wani ƙauye da ke da tazarar ‘yan kilomitoci da Mokwa, ta fuskaci musgunawa da tozartawa a cikin jama’a da zargin wai ita mayya ce.

Hassan Patigi yana nuni a bainar jama’a

Wani wanda shi ma tsautsayin ya shafa, Alhaji Saba Alheri ya gaza cimma burinsa na warkewa daga cutar ido wato (glaucoma). Pa Alheri, ɗan shekara 76 a duniya, bayan da ya idar da sallar la’asar yayin da WikkiTimes  ta ziyarceshi. Ɗan rahotonmu ya ci karo da shi na zaune a kan kujera yana jan cazbaha.

Alheri yana zaune a cikin ɗakinsa yana jan cazbarha / Hoto: Yunusa Umar

“Na sha zuwa cibiyar malamin domin neman jinya. Amma har yanzu babu abun da ya canza. Kawai na sallama na haƙura na bar komai wa Allah. Shi ne mai bayarwa kuma mai karɓar komai. Koma menene ya zo min, Allah na sane,” dattijon ya shaida wa WikkiTimes.

Tun da farko, malamin tsubbun ya buƙaci ahlin tsohon da su debo ruwa daga ƙauyen Rabba da ke da tazarar ‘yan kilomita da Mokwa domin ya yi amfani da wannan ruwan wajen dawo masa da ganinsa.

“Ɗaya daga cikin ‘ya’yana, Ndaba, ya yi tafiya zuwa Rabba wajajen ƙarfe 4:00 na safiya domin debo ruwa kamar yadda Hassan Patigi ya umarta, “ Alheri ya shaida mana. Amma haƙa bata cimma ruwa ba, Pa Alheri dai bai dawo ganinsa ba.

“Daga baya, Hassan ya ce idan har ganina bai dawo ba. Za a cero idon wani Bahaushen yaro a canza da nawa, amma ni kam na ƙi amincewa da hakan. Ba zan bari har sai an cero idon wani domin a sanya min ba. Me zan faɗa wa Allah idan aka ciro idon wani aka canza min”, dattijon ya faɗa.

Ya ƙara da cewa, malamin tsubbun ya yi iƙirarin da manuniya daban-daban amma dukkaninsu babu wani da suka gani a zahirance. Kuma ‘yarsa, Aisha ta tabbatar da kalaman na mahaifinta.

“A ƙalla, mahaifina ya ziyarci Patigi har sau huɗu, sai daga baya ya ce mu je mu debo ruwan rafi. Babu wani abu daga cikin abubuwan da ya faɗa mana da ya zo ya faru ko wani canji da muka samu,” Aisha ta shaida. 

Al’ummar ƙauye na sauraron Patigi yayin wani gangamin da ya shirya

Glaucoma cuta ce da ke haifar da makanta a duniya. A shekarar 2017 cutar Glaucoma ta kasance a gaba-gaba wajen janyo makanta a duniya da Najeriya ke da kaso 16.7 cikin 100, a cewar Dakta Adeola Onakoya, shugaban kula da cutar glaucoma kuma mai riƙon muƙamin shugaban tsangayar sashin kula da lafiyar ido na asibitin koyarwa ta jami’ar Legas, Idi-Araba. A cewar rahoton hukumar kula da lafiya ta duniya (WHO), kusan mutum miliyan 8 ke fama da cutar glaucoma a faɗin duniya da hakan ya kai ga zaman cutar ta huɗu da ke janyo cutar makanka a duniya baki ɗaya. Glaucoma na da wuyar warkuwa, amma har yanzu Patigi na iƙirarin cewa zai iya warkar da ita.

Malamin tsubbun kamar yadda WikkiTimes ta gano, ya kan shiga tsakiyar mutane ɗaruruwa, yayin da zai nuna wa mutane yatsa kuma wasu sai su fito da iƙirarin cewa sun warke daga cutar da ke damunsu sakamakon nunasu da hannu da ya yi, inda shi kuma zai kasance mai murna da annashuwa. Hakan ya kan sanya sauran jama’a su ɗauka cewa da gaske an warkar da mutanen ne, sai dai wasu na ganin kamar haɗa baki yake yi da irin waɗannan mutanen domin kau da hankalin jama’a da musu rufa ido. Yadda yake gudanar da aikinsa na nuna ya warkar da masu cutuka, mutane da dama suna mamaki da nuna kokonto kan yadda hakan ya wakana. Mohammed Ibba ɗaya daga cikin mutanen da suke shan mamakin aikin malamin, ya ce, shi kam bai warke daga cutar da ke damunsa ba duk da ziyartar malamin sau da dama.

Hassan Patigi yayin da ke tsaye cikin mutanen da ke fama da cutuka da ke neman jinya

Mahaifiyar yaron, Yalami Ibba ta shaida wa WikkiTimes cewa ɗanta ya sha fama da jinya na tsawon shekaru na yin magana da rashin tafiya.

“Na ziyarci malamin a wurare daban-daban domin neman taimakonsa. Har ma lokacin da da na je wajen Fasto Enoch [Adeboye] da wasu wurare domin neman taimako, amma har yanzu lalurar na damun ɗana.”

Ta ce, basu da ƙarfin tattalin arzikin da za su iya ɗaukan yaronta zuwa asibiti domin masa jinyar da ta dace, ta yi ƙorafin cewa shi kansa mahaifin yaron shi ma na fama da nasa matsalar.

“Sakamakon matsalar kuɗi da muke da shi da ba za mu iya zuwa asibiti ba, mun gwammace mu je wajen Mallam Hassan a Mokwa da aka fi saninsa da mai warkar da jama’a. Amma abun takaici har yanzu duk da yin dukkanin wasu dabarbarunsa na bada lafiya, ya kasa warkar da ɗanmu, ɗanmu har yanzu ba ya iya tafiya ko magana.”

Patigi Ya Sha Alwashin Ɗaukan Nauyin Talakawan Mutane Zuwa Aikin Hajji, Amma Damfara Ce Kawai 

Tsakanin shekarar 2020 da 2021 lokacin da annobar korona ta kunnu kai, hukumar kula da alhazai ta ƙasa ta bayar da adadin kujerar zuwa Hajji taƙaitattu, amma har yanzu Patigi na alwashin zai ɗauki nauyin wasu mutane zuwa gudanar da aikin hajji.

Wallafawa a turakar Facebook kan yadda Patigi ke aikin bada lafiya ga jama’a

Mohammed Usman Ndarifun, shugaban makarantar koyar da fina-finai a Lade, ya shaida yadda ta kaya da shi kan ƙaryar da Patigi ya masa na zuwa Hajji.

“Malamin ya kirani ya min alƙawarin zuwa hajji, ciki har da babban limami da wasu mutane. Mun kai mutum sama da 26 da ya mana alƙawarin kujerar zuwa Makka. Ya kuma umarceni da na faɗa wa kowa da kowa cewa zan tafi aikin hajji a Makka. Amma ya faɗa mana waɗanda suka ci sa’a za su biya kuɗin fom ɗinsu.”

Ndarifun ya ce, shi da ‘yan tawagarsa ba su sayi fom ɗin ba, amma wasu ‘yan ƙauyen da dama da aka musu alƙawarin zuwa hajji sun sayi fom ɗin daga kan kuɗi naira N500 zuwa N20,000.

Fom ɗin kujerar hajji /Daukan Hoto: Yunusa Umar

Kazalika, malamin ya gayyaci dukkanin waɗanda suka sayi fom ɗin da su je Illorin a inda za su shiga jirgi su wuce kasar Saudiyya.

Ndarifun ya ce, shi bai bi sauran mutanen zuwa Illori ba saboda kwamacalar da ke cikin gayyatar. A cewarsa, waɗanda suka yi tattaki zuwa Illorin a maimakon a basu tikitin shiga jirgi don zarcewa zuwa Saudiyya sai aka ba su wani abu a cikin baƙar leda. Aka ce musu da basu tabbacin cewa baƙin ledar za ta sauya ta dawo kuɗi da za su yi amfani da shi wajen biyan kuɗin tikitin shiga jirgi.

Mata na riƙe da baƙar ledar da aka basu da zai canza zuwa kuɗi

Wani ma da wannan tsautsayin ta rufta da shi, Mohammed Ndagi, mai shekara 60 a duniya, ya biya kuɗi naira N20, 000 domin sayen fom ɗin. Ɗansa ne aka yi wa alƙawarin zuwa hajji a lokacin da ya ziyarci cibiyar zo ka warke na farat ɗaya ta Hassan Patigi. Amma ɗan nasa sai ya so baban nasa ya yi amfani da wannan damar domin zuwa hajjin tun da bai taba zuwa ko sau daya a rayuwarsa domin sauke farali ba.

“Ina daga cikin waɗanda aka yi wa alƙawarin kujerar hajji da muke je filin jirgin Illorin kuma muka shafe tsawon kwanaki bakwai a wajen. Daga baya aka fatattakemu daga harabar filin jirgin ma baki ɗaya. Mun je sansanin alhazai da daddare domin mu gana da mutumin wato Mallam Hassan amma ya ce ba za mu haɗu da shi a Illorin ba. Amma kwata-kwata ba mu gansa a Illorin ba duk da cewa mun yi ta kiransa a waya sau tarin yawa.

Bayan shafe mako guda a Illorin, mutumin ya zo amma babu wani bayanin arziki da ya musu. Illa ya ce musu baƙar ledar da aka bai wa kowa, ya ɗauka ya je gidansa ya ajiye har zuwa lokacin da baƙar ledar za ta dawo kuɗi, inda ya basu tabbaci a kan hakan da cewa su je su ajiye a cikin gidajensu ledar za ta dawo kuɗi.

 “Ina daga cikin waɗanda aka bai wa baƙar ledar da cewa cikin mu’ujizanci za ta dawo kuɗi,” Ndagi ya shaida wa WikkiTimes.

Alhazan da aka buƙaci su riƙe leda

Cikin fushi mutumin ya bar Illorin, inda dattijon ya ce irin wahalar da suka sha ba za su taɓa mancewa da irin mummunar aikin Hassan Patigi ba.

 Farooq/ Daukan Hoto; Yunusa Umar

Umar Farooq, wani dattijo ne da ke zaune a ƙauyen Lade da ke jihar Kwara, ya samu kansa cikin mutanen da aka musu karyar samun kujerar Makka daga wajen Hassan Patigi. Ya ce, lokacin da aka zaɓeshi ya ji daɗi ya murna amma daga baya farin ciki ya koma bakin ciki.

Daga baya, aka sanar da Malam Farooq cewa zai biya dubu N30,000 domin ya samu fom, amma ya nuna cewa bai da halin da zai iya biyan wannan kuɗin. A matsayinsa na manomi tara irin wannan kuɗin abun wahala ne a gareshi. Ya roƙi tawagar Hassan a maimakon ba shi kujerar Hajji, su ba shi kyautar naira N500,000 kawai da zai fara kasuwanci domin taimaka wa iyalansa, amma abun takaici tawagar Patigi sun kasa masa hakan.

A lokacin Hassan ya cigaba da zambar mutane da yaudararsu da cewa zai samar musu da kujerar zuwa hajji duk kuwa da cewa hukumomi a ƙasar Saudiyya sun sanya takunkumin taƙaita masu zuwa hajji.

Fatima Mohammed, ita ma ta shiga cikin tsautsayin tare da mijinta, inda suka faɗa hannun ‘yan damfara su Patigi. Ma’auratan sun biya naira dubu N40,000, da nufin za su tafi aikin hajji a tare da mijinta. Fatima, ‘yar shekara 48 a duniya, matar aure ce kuma suna da danganta da Hassan Patigi, ta ce, mahaifiyarta ta faɗa cikin tarkon damfarar malamin.

Fatima a cikin gidanta /Hoto: Yunusa Umar

“Na tafi zuwa filin jirgin Ilorin tare da wasu da aka yi mana alƙawarin zuwa aikin hajji, a cikin ayarina, akwai mijina da ɗa na.

“Mun je Ilorin, amma ba mu tafi Saudiyya ba,” ta tabbar da cewa sauran waɗanda suka shiga tarkon an ba su baƙar leda da su dawo da ita gida.

Fom xin Hajji da aka bai wa mutane /Hoto: Yunusa Umar

Mutane da dama da lamarin ya shafa sun shaida wa WikkiTimes irin ɓacin rai da baƙin cikin da suka samu kansu a ciki sakamakon yadda ya yi amfani da ɗaya daga cikin ibadojin addinin musulunci yana zamba da yaudarar mutane gami da azurta kansa da kuɗin fom ɗinsu.

Yadda Ya Zambaci Mata Da Dama Ya Kwace Musu ‘Yan Kwabbai

Ɗan rahotonmu ya zanta da wasu da yaudarar Patigi da dama ta shafa, musamman matan da suke fama da lalura ta haihuwa inda malamin ya yaudaresu ya galabaitar da su.

Irin waɗannan da abun ya shafa sun haɗa har da Maryam Umar, inda ta yi bayanin yadda ta sha wahala da yaudara da zamba daga wajen Patigi.

“Mata da dama sun yi ta kawo masa Buredi a matsayin kyautarsu gareshi domin ya taimaka musu wajen samun lafiya.

“Na kawo masa Buredin naira 300 lokacin da muka ziyarceshi ni da mijina,” Maryam ta sanar da WikkiTimes. Ta yi bayanin cewa ko kadan ba ta nadamar bashi kudin ba, domin mijinta ya bata naira N11,000 kafin su bar gida.

“Kuɗinmu da muka bai wa malamin bai dawo ba har yanzu kuma har zuwa yanzu ban samu juna biyun da nake nema ba,” cewar Maryam.

Wata ma da lamarin ya shafa, Fatima Mohammed, wacce ta shafe kusan shekara goma da aure amma Allah bai azurta ta da samun haihuwa ba, ta yi bayanin irin ƙuncin da Hassan Patigi ya kara jefata ciki.

Fatima, tana zaure na ɗakinta /Mallakin Hoto: Yunusa Umar

Matan da ke fama da matsalar rashin haihuwa na buga-bugar nema wa kansu mafita, inda suka tsinci kansu a yayin da aka buƙaci su nemi taimakon Patigi domin fita daga cikin yanayin da suke ciki, sai dai a maimakon samun taimako, sun tsinci kawukansu a yanayin damfara da kwace musu ‘yan kwabbai. Fatima ta sha gwagwarmar neman taimako a wajen Patigi amma ba ta samu nasara ba.

“An faɗa min cewa matan da basu samu haihuwa ba za su iya samun taimako ta yadda za su samu juna biyu idan suka ziyarce shi,” ta shaida. Ta qara da cewa bisa mu’ujizar da ake ta basu labari na mutumin, ya sa suka yanke shawarar zuwa gareshi ita da mijinta domin neman taimako.

“A lokacin da ni da mijina muka je cibiyar Malam Patigi, mun biya naira dubu 10. Ya ce mu ba shi kudin mu tafi, muddin ban samu juna biyu ba mu dawo zai maida min kuɗina,” matar ta shaida.

Ta ce, juna biyu dai kam bai samu ba, duk da ziyara da suka kai wa malamin sau tarin yawa, kuma dukkanin kuɗaɗen su da suka bai wa malamin ba su dawo ba har yanzu.

Wata ma, Fatima Jibrin, ta bada labarinta, wacce ta fito daga ƙauyen Sakpefu a jihar Kwara, da ta je Mokwa neman agaji da taimako daga wajen Patigi.

Fatima/Mai Hoto: Yunusa Umar

Da take laburta yadda ta kaya, “Na yi tattaki zuwa Mokwa na zauna a can har na tsawon mako guda. Na fahimci yadda yake gudanar da ayyukan tsubbunsa a lokacin da na je Mokwa.”

“Mijina ya biya naira dubu 10, ni da wasu matan da ke fama da lalurar haihuwa mun yi ta bada kudinmu,” ta shaida.

  Mata Masu neman haihuwa ke kirga kuɗi

“Bayan da muka gama ƙirga kuɗin, ya umarci mu koma gidajenmu mu jira abun da Allah zai yi,” matar ta shaida.

Daga nan ta ce, malamin ya umarceta da ita da mijinta da kada su sake saduwar aure har na tsawon wata guda.

Matar ta cigaba da cewa, duk da malamin ya kwashi kuxaxe daga wajen mijinta, amma har yanzu ba ta samu juna biyu ba, duk kuwa da cewa sun bi matakan da Patigi ya gindaya musu.

Umar Hawawu, ‘yar shekara 40 wacce ta fito daga ƙauyen Patigi a jihar Kwara da ta yi aure tsawon shekara goma amma Allah bai bata haihuwa ba, ta ce, bayan rashin nasarar samun juna biyu daga wajen Patigi, sai da ta san hanyoyin da ta bi ya dawo mata da naira dubu 11 da ta ba shi.

Matar auren a gidanta /Hoto: Yunusa Umar

“An ce min wasu kurame, makafi suna warkewa daga wajensu kuma wasu na samun haihuwa, amma ni dai ban ga irin waɗannan ba.”

Mata da dama masu neman haihuwa sun shaida cewar sun ziyarci Patigi sun kuma ba shi kuɗaɗe amma har yanzu ba su samu juna biyu ba kuma malamin bai dawo musu da kuɗaɗen su ba.

Yadda Ya Sanya Mata Tsirara A Bainar Jama’a Da Zargin Maita

A ranar 23 ga watan July, dan rahotonmu ya ziyaci ƙauyen Bukka, da ke da tazarar ‘yan kilomita ƙalilan da Mokwa domin ganawa da wata tsohowar matar da aka zarga da kasance Mayya a babban makarantar Nazari da Firamare ta Mokwa (Yeko Rabba).

A lokacin da ɗan rahoton ya isa gidan Nnaba dattijowar matar da Hassan Patigi ya zarga da cewa mayya ce, wani da ke sayar da mai na ‘yan bunburutu a ƙauyen, ya shaida ma wakilinmu cewa Nnaba ta rasu.

“Ta rasu, ba da jimawa ba bayan da ta dawo daga Mokwa.”

Da ɗan rahoton namu ya nemi zantawa da iyalan mamaciyar, ya hanasa damar hakan, bayan nacewa, ya nuna wa dan rahoton namu wani dan uwan mamaciyar mai suna Alhaji, inda shi kuma dan uwan nata ya ki bada bayanin abun da ya faru da ‘yar uwan tasa.

Ya ce, ya mance abubuwan da suka faru kuma sun bar lamarin ga Allah.

Kafin mutuwarta, tsohowar matan ta sha fama da cutukan da suka shafi na sanyi a jikinta, inda Nnaba ta ziyarci malamin domin neman taimako kan cutar da ya jima a jikinta, amma sai ya zargeta da maita ya kuma musguna mata a bayyanar jama’a.

“Cikin hanzari, da na fahimci ‘yar uwata ta ziyarci Mokwa domin ganin malamin kan rashin lafiyar da take fuskanta, shi Malamin Hassan Patigi ya zargeta da maita. Na kira wani a Mokwa na roƙeshi da ya yi ƙoƙarin cetota daga fusatattun mutane, cikin yardar Allah ta dawo gida a raye,” ya shaida.

   Dattijowa Nnaba wacce take fama da ciwon sanyi da malamin ya zarga da cewa mayya ce.

Pategi ya buƙaci matar da ta amince cewa ita mayya ce, amma ta ƙi amincewa da hakan.

Ɗan uwan mamaciyar ya li bada cikakken bayani kan yadda ta rasu, inda ya yi nuni da cewa iyalanta sun bar lamarin ga Allah wanda shi ne mahaliccinta.

Dukka a wannan shekarar, Hajiya Hawau Umar, wacce take fama da ciwon rheumatism a kafaɗarta, ita ma Patigi ya zargeta da Maita. Dakarun Pategi sun yi tsirara wa matar da nufin cire mata cutar ciki har da duka.

Matar daga bisani ta shaida wa WikkiTimes cewa ta je cibiyar Pategi ne domin neman lafiya daga ciwon da ke mata zafi, sai dai daga nan kuma aka zargeta da maita da kokarin kashe sarki.

Surukin matar, Kawu Sadu, wanda ya yi magana a gabanta, ya yi bayanin abubuwan da suka faru daki-dai da cewa, matar ta je neman taimako daga cutar da ke damunta a kafadarta na hagu.

Ya ce, a maimakon a samar mata da magani kawai sai ya zama an zargeta da kokarin kashe sarki da cewa ita mayyace.

“Hassan ya je fadar Etsu Umar Bologi II domin duba zallar iyalan sarkin, amma Hajiya tana bakin kofar fadar,” Sadu ya yi bayani. Wani mai tsaron Hassan wanda ya yi alkawarin shirya zaman, ya ja-ta zuwa cikin fadar.

Ba kamar ma sauran waxanda lamarin da abun ya shafa ba da suka yi magana a xan firgice Hajiya Hauwau Umar kai tsaye cikin kwarin guiwarta ta shaida wa WikkiTimes yadda ta kaya da ita, ciki har da karya da qage da shi Patigi ya sharara mata a gaban Sarkinsu.

Duk da kariyan kai da ta yi, Hassan ya zargeta da cewa ita Mayya ce, kuma ya umarci masu gadinsa da su tsareta. Kazalika, Sarkin sai ya shiga cikin lamarin a wannan gabar tare da umartar a saketa tun da ta ce ita ba mayya ba ce.

A hanyarta (Hauwau) na fita daga fadar, masu tsaron Hassan Patigi sun kwace mata waya tare da hanata tuntubar iyalanta da ahlinta. Ta bayyana yadda masu tsaron malamin suka yi mata tsirara, inda masu tsaron nasa, sama da bakwai suka yi ta watsa mata ruwan leda a jikinta. Kama-kama a wannan wajen a wannan matakin har suka kai ta zuwa ga zama tsirara sakamakon musgunawarsu da kuma watsa mata ruwa da suka yi ta yi ba kakkautawa, duk da kayan jikinta sun yi kasa bisa dole haka jami’an tsaron Patigin suka ci gaba da watsa mata ruwa.

   Yadda suka yi wa Hajiya Hawau tsirara

Bugu da kari kan lamarin Hauwau, Hassan Patigi an bada labarin yadda yake zargin mutane da daura musu laifin cewa mayu ne wanda hakan ya kan kai ga tauye wa bil-adaman hakkinsu da musguna musu iyaka hadi da sanya su abin kyama a cikin al’ummar da suke yi, kana hakan na jefa zargi da rashin fahimtar juna a tsakanin mutane da daman gaske, muni kan wannan, ayyukan nasa na kai wa ga azabtar da wadanda suka zarga da maita da kuma kuntata musu, kamar yadda WikkiTimes ta gano. Kuma, mutanen da lamarin ya shafa da ake zargi, a wasu lokutan ana samun yanayin da ake dambatuwa da sanya karfi na duka ga mutane. Lamarin na janyo tashin hankali da take hakkin bil-adama da hakkokinsu na rayuwa da sunan zargin maita da shi Hassan ke yi.

A ranar 20 Disamban 2017 majalisar dokoki ta kasa ta amince da kudirin yaki da azabtar da mutane, wanda har shugaban kasa a wancan lokacin Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu. A cikin dokar, nau’ikan yi wa mutane tsirara na shiga layin azabtarwa. Idan aka kama mutum da irin wannan laifin zai iya shafe shekara 25 da a gidan yari.

Hauwau, wacce lamarin ya shafa bayan shan fama da musgunawa. Ta koma gidanta, inda ta sake fuskantar wasu sabbin qalubalen sakamakon yadda al’umma da makwabtanta ke tsangwamanta da zarginta kala-kala wanda har hakan ya shafi iyalanta.

Ta cigaba da cewa, “Jikina ya tsanatanta har ma ya shafi yadda ‘ya’yana suke ji.” Ta ce, tun daga wancan lokacin da aka mata titsiye da azabtar da ita har suma sai da ta taba yi kuma jinya a kai a kai take yi sakamakon yadda jikinta ya yi tsanani.

Bayan tsayuwar daka da aka yi da nuna wa Patigi illar musguna wa matar, ya fito a bayyanar jama’a ya bayar da hakuri da neman gafararta.

 Maganin da aka nuna /Hoto: Yunusa Umar

Kazalika, ta bayyana yadda ta fara samun sauki tun lokacind a ta maida hankali wajen amsar maguna daga wajen kwararren likita a asibiti dangane da ciwond a ke damunta. Sannan, ta gode da yaba wa kokarin da Malam Sanusi Lafiagi bisa dagewar da ya yi har hakan ya sanya Patigi fitowa duniya wajen neman gafararta.

Usman Salihu, mai sana’ar daukan hoto ne wanda a baya ya yi aikin daukan hotuna ga shi malamin tsubbun, ya tabbatar wa jaridar nan cewa, mutane da dama da suke fama da cutuka da suka ziyarci malam Patigi ba su samu lafiya ba duk da karerayin da malamin ya musu da ‘yan dabarbarunsa.

“Ba ya iya samun damar warkar da mutane. Duk wanda ya fito ya ce muku ya samu lafiya sakamakon aikin Patigi karya yake yi.” A cewar Salihu, malamin ya kasance wani mutum mai abubuwa kamar marar cikakken hankali, inda ya nuna damuwarsa kan yadda jama’a ba su gane irin tuburan xin haukan da malamin ke fama da shi ta hanyar ayyukansa, dabi’unsa da lamuransa.

Salihu, ya ce, ya cimma matsayar ficewa daga ayarin Patigi ne tun lokacin da ya ga yadda mutum ke azabtar da mata da shokin a cibiyarsa bisa zarginsu da Maita.

Wata Tsohowar Mata da aka azabtar da abun shokin

“Ya azabtar da wata dattijuwa a gaba har sai da ta fita cikin hayyacinta,” ya nuna damuwarsa, kan yadda Patigi ke tarawa ko kasancewa a kewaye da wasu gurbatattun mutane da yake turawa cikin jama’a domin su yi basaja kana su fito cikin jama’a su nuna cewa sun warke daga cutar da ke damunsu alhali aiki suke yi masa domin janyo hankalin mutane da yaudararsu da su zo gareshi.

Salihu ya kara da cewa, “Shi din malamin da ke bayar da magani ne a Liberia kafin ya koma Mokwa domin damfarar jama’an da basu ji ba su gani ba kana ya musguna musu, ya azabtar da su kuma ya tara kudi daga wajensu.”

Katin Shaidar kasancewa dan kasar Liberia Na Patigi

Salihu ya ce, Hassan Patigi, ko karatun Alkur’ani bai iya yi amma yana ikirarin cewa shi malami ne.

Cibiyar warkar da mutane ta Patigi /Hoto: Yunusa Umar

Yadda Ya Musguna, Ya Azabtar Da Mutane Da Tauye Musu Hakki, Waxanda aka zarga da maita sun yi bayani

A ranar 2 ga watan Agustan, wakilinmu ya yi tattaki zuwa Lachi, kauye ne da ke Enagi a karamar hukumar Enagi da ke jihar Neja, domin bincike da ganawa da wasu mutanen da aka zarga da kasancewa Mayu.

Mohammed Abubakar, uba ne da ke da ‘ya’ya da dama, da aka zarga da kasancewa Maye an kuma tilasta musu yin fitsari a bakin junansu, ya yi qarin haske ga WikkiTimes kan yadda aka zargeshi da maita.

“An yi min karya. Ba ni kadai ne aka zarga da kasancewa Maye ba,” ya shaida.

“Ya zarge mu ya gurfanar da mu,” sai dai ya kasace yin wasu cikakken bayanin da aka nema domin tsoro da fargabar abun da ka iya jewa ya dawo.”

Hassan dai idan ya samu mutanen da ya laka musu zargin maita na jansu zuwa cibiyarsa domin neman cewa zai cire musu maita ko sanya zargi da haxasu rigima da mutane. Lamarin da ke janyo fitina da yanayi a wasu lokutan har azabtar da mutane da musu tsirara yake yi da sunan maganin cire maita.

Wani Mutum da aka zarga da cewa Maye ne /Hoto Yunusa Umar

“Ban je wani asibiti ba. Ina zuwa wajen likitoci ne kawai idan na ji bana da lafiya, a lokacin da na kamu da rashin lafiya a Mokwa bayan faruwar lamarin na shafe tsawon shekara ina jinya.” Hakan ya ne sani zuwa asibiti domin amsar wasu allurai.”

“Ba na iya kallo da ido daya, ina iya yi da guda. Amma ina jin zafi sosai a cikin jikina yanzu,” ya shaida. “Lokacin da ya bukaci mu tafi, ya umarceni da na yi fitsari a bakin wanda yake kusa da ni.”

“Da na faxa masa cewa ni fa bana jin fitsari, sai ya ce min karya nake yi sai ya ce ma wanda yake kusa da ni din ya yi fitsarin a bakina. Wasu mutane sun bugeni sun daddakeni da sanduna,” ya shaida.

Duk da irin wannan ta’asar, babu wata kungiya da ta fito ta tsaya wajen kare mutanen da ake musguna musu da cutar da su balle ma a nema musu adalci daga wurin wannan malamin.

Har Sarauta Wasu Sarakuna Suka Bai Wa Patigi

Hassan ya kasance mai zubar wa mata mutunci da kima ta hanyar azabtar da su da musu tsirara a bainar jama’a. amma duk da hakan wasu sarakuna sun gamsu da danyen aikin da ya ke yi wajen cutar da jama’a da sunan yaki da Mayu.

A misali, al’ummar Kutigi da ke jihar Neja har nadin sarauta mai suna Mukadami basaraken yankin Alhaji Hussaini Abubakar Woncin (Ezonuwan) ya ba shi.

Ya samu nadin sarautar ne domin lullube danyen aikin da yake yi na cutar da jama’a da azabtar da su.

 Hassan Patigi tare da sarkin Kutigi

A cewar wani wallafa da wani hadiminsa a bangaren yada labarai ya wallafa a shafin Facebook, Idris Gana, ya ce, “Hassan Patigi daga yau Juma’a 28th of August 2020, Mayun da suke yankin Kutigi sun gamu da gamansu za su gana, za su arce cikin dare su gudu ba za su sake samun damar kashe wani ba.”

Kazalika, basaraken Patigi, HRH Alhaji Ibrahim Umar Bologi, ya nada shi mukamin Sarki Mallami amma daga baya an warware masa rawanin bayan da aka gano shi malamin bogi ne da ke karyar warkar da mutane.

 Bologi, Sarkin Patigi

Majiya daga yankin na cewa, “An kwace mukamin da aka basa saboda Sarkin ya gano cewa shi malamin bogi ne.”

Dr Leo: Ya Yi Kira a cafke Malamin Bogin

A hirarsa da WikkiTimes, Dr. Leo Igwe, mai rajin kare hakkin bil-adama na kasa da kasa, ya bukaci hukumomi da su cafko masu aikata irin wanan danyen aikin domin gurfanar da su.

         Dr.Leo Igwe

Ya ce, dole ne a yi tir da azabtar da jama’a da sunan wai su mayu ne, inda ya ce dole ne a tashi tsaye a magance wannan matsalar domin kauce wa jefa jama’a cikin fitina.

A hira da Abdullateef Lanre Abdullahi da aka fi sani da (Ibn Abdillah As-sudaisiy Al-Iloori), malamin addini kuma mai sharhi kan lamuran yau da gobe kana kwararren lauya ne, ya ce, ba daidai ba ne wani mutum ya kira kansa da cewa shi mai mai warkarwa.

“Babu wani baya ga Allah da zai ce maka shi mai warkar da masu fama da cuta ne,” ya kuma ce babu wata nau’in cutar da babu maganinta da aka tanadar.

Abdullahi, ya shawarci jama’a da su ke zuwa asibiti domin duba lafiyarsu a duk lokacin da suke ciki wani jarabawar rashin lafiya ba wai zuwa gurin malaman karya da za su ke jefa su cikin fitina ba.

Hassan Patigi tare da matayensa

Abubakar Kpada, likita ne da ke aikin gwajin juna biyu a Patigi da ke Kwara, da ake damfara, ya yi bayanin cewa ba shi ne shugaban likitoci na cibiyar ba, inda ya yi bayanin cewa wasu matan da ake gwadawa da a ce suna dauke da juna biyu amma ba su haihuwa a zahirance ko a ga cikin ya bayyana a bayyana, ya ce, wannan kuma lamari ne na Allah.

Sai dai ya kasace tuna nawa ne aka amsa domin yi wa mata gwajin juna biyu da za a gano suna dauke da juna biyu amma in sun tafi sai a ga ba su da shi.

Yaswasu, wani ma’aikacin jinyar ne na daban da ke gwajin juna biyu a Mokwa ya shaida wa WikkiTimes cewa gwaje-gwaje da dama da ake yi suna nuna cewa matan na xauke da juna biyu amma ba za a samu karin haske a kai ba. Ya misalta sakamakon haihuwa da iko ne na Alah.

Ya ce, naira 500 suke amsa wajen gwaji, inda wasu matan ake gano suna xauke da juna biyu amma wasu kuma a samu ba su da shi, sai dai ya kasa bayar da cikakken bayani kamar yadda aka nema.

Da ya ke maida martani kan waxannan zarge-zargen, Malamin da ke ikirarin warkar da masu cuta, Hassan Patigi, ya bayyana cewar nan ba da jumawa ba wakilinmu zai shaidi yadda za a gano wasu masu xauke da maita da dama.

Ya ce, zai cika alkawarin da ya xauka na cewa zai tura mutane zuwa kasar Saudiyya domin sauke farali a watan Janairu.

“Shirin aikin hajji na kan gudana, da izinin Allah zan cika alkawarin da na dauka. A kowani lokaci daga watan Janairu zuwa Fabrairu.

A lokacin da aka nemi ya bayar da cikakken bayani kan yadda yake gano Mayu, ya tsara cewa zai amsa wannan bayanin da karfe 8 na dare, amma ya xage tattaunawar zuwa 10 na dare, da cewa yana ganawa da baki, “Mu bar ganawar zuwa 10 domin mu samu wadataccen lokaci mu tattauna,” sai ya kashe wayar.

Da aka sake nemansa a karo na biyu, Hassan Patigi ya ce fom xin da aka sayar na zuwa Makka ba nasa ba ne domin shi fom xinsa kyauta ake rabarwa.

Ya ce, “A lokacin da na ziyarci Ogun, wasu jami’an tsarona sun buga takardun fom masu kusan kama da nawa domin sayar wa jama’a. ni bana da hannu a ciki domin ni fom xina kyauta nake rabarwa. Lokacin da na dawo na fahimci wannan, na gargadi dukkanin wani kan sayar da fom,” ya shaida wa WikkiTimes.

Da aka tambayeshi ko ya hukunta ma’aikatansa da suke sayar wa jama’a fom alhalin kyauta ya dace su basu, ya jingine tambayar a gefe, ya ce, zai cika alkawarinsa idan ya samu lokaci.

Da dan rahotonmu ya tambayeshi wasu tambayoyi da dama, sai ya yi alkawarin cewa zai amsa su daga baya domin zai saurari bakinsa.

  Hassan Patigi

Me Hukumomi Suka Ce Kan Wannan Lamarin

A lokacin da WikkiTimes, ta tuntuvi Aliyu Yahaya, Mayakin Etsu Nupe, ya nuna cewa ba su da masaniya kan aikace-aikacen Hassan Patigi a yankin Nupe. “Ban san da wani batu kansa ba,” ya shaida, tare da katse wayar ba tare da wani karin haske ba.

Aisha Wakaso, hadimin gwamnan Neja kan hdimar jarida na takarda, ya ki amsa wayar da aka yi ta masa da jerin sakonnin karta kwana domin jin bahasi daga bangarensu.

Danmaigoro Zubair Ibrahim, hadimin gwamnan jihar Kwara kan harkokin addinin musulumci, ya yi fatali da batun Hassan Patigi, “Yi hakuri nemo wani batun na dabab. Wannan ya zama tarihi. Mun shawo kan batun. ‘yan sanda sun dauki matakan da suka dace kuma sun umarceshi da kada ya sake yin irin abun da yake yi.”

Ibrahim ya ce gwamnatin Kwara ita ba ta ma da masaniyar Patigi ya shiga cikin jihar domin a cewarsa cibiyar warkar da mutane ta malamin na Mokwa ne ba wani kauye da ke Kwara ba.

Dele Oyewale, kakakin hukumar yaki da rashawa, ya shawarci dan rahotonmu da ya shigar da korafinsa ga ofishin EFCC da ke Illorin ta jihar Kwara.

Duk kokarin jin ta bakin jami’an watsa labaran hukumar ‘yan sanda a Neja da Kwara, Wasiu Abidoun da Okasanmi Ajayi, ba su amsa kiran waya da sakon karta kwana da dan rahotonmu ya aike musu ba.

Daga Yunusa Umar; Fassara, Idris Khalid; Tacewa, Ajibola Amzat

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories