NDLEA Ta Tarwatsa Gidajen Sayar Da Ƙwayoyi, Ta Kama mutane 198 A Kano

A ranar Talata, ne Hukumar NDLEA Ta Ce ta kama wasu mutane 198 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi tare da tarwatsa gidajen sayar da miyagn kwayoyi guda 21 a Kano.

 Kakakin hukumar Mista Sadiq Muhammad-Maigatari Shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

 A cewarsa, an kama wadanda ake zargin ne a tsakanin ranakun 17 zuwa 26 ga watan Janairun 2024, a ci gaba da aikin ‘Operation Hana Maye’, wanda kwamandan jihar, Abubakar Idris-Ahmad ya ƙaddamar.

 Ya ci gaba da cewa, “aikin yana ƙoƙarin yaki da safarar miyagun ƙwayoyi da kuma shaye-shayen a jihar.  Daga cikin mutane 198 da aka kama, 177 maza ne, yayin da sauran 21 mata ne.

 “A cikin mutane 198 da ake zargi, 61 daga cikinsu an kama su ne a wani kulob da a yanzu aka maida shi wurin hada-hadar ƙwayoyin.

Ya kuma ƙara da cewa hukumar ta NDLEA reshen Kano ta himmatu wajen ganin ta kawar da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da safarar su.

 “Za mu ci gaba da zage damtse wajen ganowa da kuma kamo masu safarar miyagun ƙwayoyi, da kuma ƙoƙarin daƙile hanyoyin samar da magunguna, da kuma ba da tallafin horo ga waɗanda ke yammaci da ita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories