Yadda ‘Yan Ta’adda Ke Keta Haddi Da Cin Zarafin Mata A Sokoto

A wasu kauyukan jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya, inda har yanzu gwamnati ta gaza kawo musu karshen tashe-tashen hankula da aka kwashe shekaru goma ana yi, mata da ‘yan mata sun kasance wadanda ‘yan ta’adda ke ketawa haddi. Wanda hakan ya haifar da cuwurwuka da kuma daukar ciki.

Majiyoyin yankin Isa da karamar hukumar Sabon Birni sun shaida wa WikkiTimes cewa da kyar suke barci da dare, saboda fargabar harin ‘yan bindiga. Mata da ‘yan matan da abin ya shafa suna fuskantar rauni saboda ana nuna musu wariya bisa lalurar da suke dauke da ita, ba su da karfin yin wasu ayyuka saboda rashin ingantaccen asibiti. Waɗanda ke dauke da ciki a cikin su suna matukar wahala.

“‘Yan bindiga a kauyen Tsabre mai tazarar kilomita 25 daga tsakaninsu da karamar hukumar Isa, suna yi wa mata fyade, kuma suna garkuwa da mutanen yankin, kuma har yanzu babu wani yinkuri a jami’an tsaro ke yi wajen dakile su,” Adamu Mudi, wani mazaunin yankin ya bayyana.

Fadimatu mai shekaru hamsin da uku ta kara da cewa, “Babu wanda ya isa ya hana su yin duk abin da suke so, suna da karfi sosai,” kamar yadda ta fadi wa WikkiTimes.

Fadimatu na zaune a ‘yar bukkar ta da ke kusa da wata katuwar bishiyar mangwaro dake bada inuwa a kasuwar garin.

Yayin da take magana, danta mai suna Habibu, wanda ke tafiya da sanda tun bayan da ya sami rauni sanadin harbin bindiga a kafarsa ta hagu, shi ma ya zo ya zauna karkashin bishiyar mangwaro inda mahaifiyarsa ke zaune.  Ya kara da cewa, “Matan wannan yankin sun rasa martabar su amma sai dai ba laifin su ba ne.  Saboda ‘yan ta’adda suna nuna iko akan ko wace yarinya ko mata.”

Saboda yadda abubuwa suka yi tsanani har ta kai ga ‘yan mata da matan aure suna bayar da kansu saboda tsaro da kuma kare iyalin su daga cin zarafin ‘yan bindiga.

A cewar wani dattijo a kauyen Zangon Malam, ba a kai wa hukuma rahoto saboda tsoron me zai je ya dawo.

“Wannan lamari abu ne da ya fara zama sananne ga yankunan da ‘yan bindiga ke addaba,” in ji shi.

Hukumomin yankin sun damu sosai kan yadda mata da ‘yan matan kauyukan Isa ke ba da kansu don ceton ransu da kuma tsoron a sace su.  Tsakanin yankin da cikin garin Sokoto tazarar kilomita 224 ne. Ba a fiye bin hanyar ba saboda barazanar ‘yan bindigan da ka iya dirowa a kowane lokaci, ba dare ba rana.  Kodayake wasu lokaci manyan motocin itace na bin hanyar.

A’isha suna ne da ya yi kauri sosai a bakin al’ummar wannan yanki, ta na da shekaru 21, rayuwarta ta canza a lokacin da ‘yan fashin suka zo kofar gidann su, ta yi kokarin boye ‘yar uwarta ‘yar shekara 13, amma sai suka nuna mata bindiga a goshinta, lamarin da ya kasance mata tamkar mafarki, hawaye ne ke bin kuncinta, Aisha ta roki da a dubi irin halin da suke ciki, domin suna rayuwa cikin rashin damuwa da tsoro.

“Da alama babu wanda ya damu da rayuwarmu, muna rayuwa cikin rashin tabbas, damuwa, da tsoro,” in ji ta. 

“Yan bindiga sun kashe wasu daga cikin mu saboda kin amincewa su yi lalata da su.”

Wata mata mai suna Adama Haliru mai shekaru 53 daga Sabon Birni ta rasa ‘ya’yanta mata guda biyu a sanadiyyar ‘yan bindiga, ba ma ‘ya’yanta mata kadai ba, hadda mijinta wanda aka kashe a wani hari da aka kai a watan Agustan 2021 a kokarin kare iyalansa.

“Sun kashe mijina a gabana a kokarin shi na kare mu daga daga keta haddi,” in ji ta.

Maryam ‘yar shekara talatin da takwam halin da ta shiga ya wuce tunani har a gaban ‘yan uwanta an mata fyade.  Maryam ta ba da labarin irin yadda aka tilasta mata shiga cikin dajin da ke kusa, da su inda aka yi mata abubuwa marasa dadin fada.
A martanin da gwamnati ta yi game da lamarin, daraktar mata a ma’aikatar mata da kananan yara ta Jihar Sakkwato, Hajia Habiba Ahmad, ta ce tabbas suna sane da irin wadannan lamuran amma sai dai rashin cikakiyar tsaro ga tawagar ma’aikatansu shi ya sa ba sa iya zuwa irin wadannan wurare.

“Tabbas al’ummomin wannan yanki sun shafe shekaru suna fuskantar matsalolin da suka shafi cin zarafi amma babbar matsalar ita ce rashin tsaro shi ke hana mu shiga yankunan don gudanar da ayyukan mu,” in ji ta.  

“Ba a ba mu izinin zuwa wadannan yankuna ba.”

A cewarta, ma’aikatar su tana da gine-gine a manyan kananan hukumomin jihar amma sai dai rashin tsaro ke hana gudanar da aiki yadda ya kamata a wadannan yankunan.  

Habiba ta koka da yadda ake samun yawaitar mata masu kamuwa da cututtukan da ake yadawa ta hanyar jima’i da kuma masu ciki da ba na aure ba sakamakon ‘yan bindiga da suka addabi yankunan.

Ta ce, “Wadannan matsaloli sun karu sosai fiye da saboda ko a wannan makon kadai, mun sami irin wadannan korafe-korafen kusan shida su na neman suna neman akai musu agaji”, ta kara da cewa mafi yawan wadanda abin yafi shafa sun ne ‘yan tsakanin shekaru 14 zuwa 17.

“Mun samu rahotannin yadda ake lalata da kananan yara mata kuma suna kamuwa da cututtuka irin su ciwon hanta, HIV da sauran cututtuka masu yaduwa,” in ji Habiba.

Ta bayyana cewa asibitin Maryam Abacha shi ne babban asibitin ma’aikatar da ake amfani da shi wajen bayar da agajin jinya ga wadanda abin ya shafa da wadanda suka tsira daga irin wannan lamari.

“Mun yi ta ba da magani kyauta ga wadanda abin ya shafa ciki har da wadanda aka yiwa ciki.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories