Bisa Bankaɗo Bayanan Sirri Da Wasu Ƴan Jarida Suka Yi Shugaban Kwaleji Ya Sa An Tsare Su

Ƴan sanda a jihar Kwara sun tsare babban editan jaridar Informant247 Salihu Ayatullahi da Adisa-Jaji Azeez, Editan jaridar a ranar Litinin.

 An tsare ƴan jaridar ne a garin Ilorin bayan ansa goron gayyatar da ƴan sanda suka kai musu a ranar Litinin.

 WikkiTimes ta fahimci cewa kama ƴan  Jaridar ya biyo bayan umurnin Shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kwara, Engr.  Abdul Jimoh Muhammad.

 Rahotanni sun bayyana cewa An gayyaci Salihu Ayatullahi da Adisa-Jaji Azeez da misalin karfe 2:30 na rana a yau Talata, 6 ga Fabrairu, 2024.

An gano cewar Tsare ƴan jaridar na da nasaba da wani bincike da jaridar The Informant247 ta buga a ranar 2 ga watan Fabrairu, 2024, inda ake zargin shugaban Kwalejin ya yi iƙirarin ƙarya game da halin da asusun makarantar ke ciki tare da kaddamar da ayyukan da ba a kammala ba.

Babban editan The Informant247 Bai tsaya ba ya yi saurin garzayawa babbar kotun tarayya don neman a basu kariyar da doka ta tanadar wa ƴan jarida.

 A halin da ake ciki, an shigar da kwafin aikin da aka yi wa alama mai lamba FHC/IL/C5/14/2024 a ofishin rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kwara

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories