Ana Shirye-shiryen Haramta Amfani Da Shafin Tiktok A Amurka

‘Yan majalisar Amurka zasu kada kuri’a a yau Laraba game da dakatar da kafar sada zumuntar ta Tiko-tok a fadin kasar, da nufin tilastawa kamfanin barranta kansa da China matukar yana sha’awar ci gaba da zama a Amurka.

Wannan dai yana nuna irin karfin da kafar Tik-tok din mallakin China ke da shi.

Tuni China ta bakin ministan harkokin wajen ta Wang Wenbin ta yi watsi da wannan shiri na Amurka, tana mai cewa babu abinda zai yi illa yiwa Amurkan da ‘ya’yanta illa.

Amurkan na zargin kamfanin na Tik-tok da zama barazana ga tsaronta da kuma yi mata kutse a rumbunan adana muhimman bayanai, duk da dai bata bayar da wata shaida game da hakan ba.

Wang ya ce wannan dabi’a ta Amurka ba zata kara mata komai a wannan lokaci ba illa nunawa duniya karara yadda take kokari wajen dankwafe duk wata kasa da ta zo da abinda duniya ke maraba da shi, inda bai ta bace ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories