Hotuna: Kanawa Na Gangamin Dasa Bishiya Miliyan Ɗaya

Kwararowar Hamada da dumamar yanayi na daga manyan batutuwan da yanzu haka suke daukan hankalin gwamnatoci da kuma kungiyoyin kasa da kasa, sakamakin irin illolin da suke da su, musamman ma ga albarkar kasar noma.

Dasa bishiyoyi na daga muhimman matakan da ake dauka domin rage tasirin kwararowar hamadar a daidai lokacin da ake fama da sauyin yanayi da yanzu haka ya addabi duniya.

A irin wadannan matakan ne wani matashi a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya, Ismail Auwal ya fara wani shiri na dasa bishiyoyi guda miliyan ɗaya a jihar Kano.

Mafi yawan ‘yan Nijeriya suna sare da kuma Kona bishiyoyi, duk da dimbin iskar gas din da kasar ke da ita, wacce yanzu haka mafi yawancin ta na bin sararin subhana ne kawai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories