Sharrin Ƙungiyanci A Addinin Musulunci

Wato babban dalilin da ya sa na ke nisantar kungiya kowacce iri a musulunci shine mummunar halayyar da ta ke saka akasarin mabiya a ciki. Wato duk wanda kake adawa da kungiyarsa ba za ka iya masa adalci ba, duk kyawon abinda ya yi ba zai burge ka ba, sannan kuma duk munin abinda naka ya yi, zaka fito ba kunya ka kare shi, saboda sunan akida.

Wannan halayya kuma ta ci karo da ginshikin musulunci a Qurani da koyarwar manzon Allah tsawon rayuwarsa. Allah fa cewa ya yi

Q4:135 “Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kasance mãsu tsayuwa da ãdalci, mãsu shaida sabõda Allah, kuma kõ dã a kanku ne kõ kuwa, mahaifa da mafi kusantar zumunta, ko (wanda ake yi wa shaida kõ a kansa) ya kasance mawadãci kõ matalauci, to, Allah ne Mafi cancanta da al’amarinsu. Sabõda haka, kada ku bĩbiyi son zũciya, har ku karkata. Kuma idan kuka karkatar da magana, kõ kuwa kuka kau da kai, to lalle ne Allah Yã kasance Masani ga abin da kuke aikatãwa”

Adalci wajibi ne ka yi shi a kan kowa idan har tarbiyar musulunci ta ratsa ka. Babu son da ya wuce na karan kai, mahaifa da makusanta, amma Allah ya wajabta mana yin adalci ko da a kan su ne. A rayuwar manzo mun tuna sanda wata yar babban gida ta yi sata a madina wasu sahabbai su ka zo neman kamun kafa kada a yi mata hukunci, hankalin Annabi ya ta shi, ya yi rantsuwa cewa ko fatima ce ta yi sata, sai ya zartar mata da hukuncin Allah. Wannan shine adalcin da wannan aya ta wajabta, kuma Annabi ya koyar a wannan hadith. Haka nan adalci wajibi ne ko a kan wanda ba addininku daya ba, ballantana wanda kuke addini guda. Lokacin da sojojin Musulmi suka kama Birnin Kudus, da Umar ya zo ana zagayawa da shi, a daidai cocin Holy Sepulchre, coci mafi mahimmanci a kiristanci inda aka fara binne Isa bayan gicciye, sai lokacin sallah ya yi kuma gwamnan Jerusalem, Sopronius ya nemi ko Umar zai yi sallah a cikin cocin? sai Umar ya ki, tare da cewa yana tsoron idan yayi sallah a ciki musulmi zasu iya kwace cocin su maida shi masallaci kuma hakan zai raba kirista da wajen bautarsu mafi mahimmanci. Adalci ke nan, kuma wajibi ko akan wanda ba musulmi ba.

Duk mai imani, ba zai so ya ga ko kafiri ana masa kisan gilla ba, amma wata uku ana kashe yan uwanmu Falasɗinawa amma musulmin duniya sun kasa haduwa su tsayar da lamarin. A jiya Iran ta kai farmaki Isra’ila, abinda har wadanda ba musulmi ba da mulhidai na na’am da murna da yunkurin. Amma wasu yan uwanmu saboda muguwar akida ta izalanci sai sukar kokarin na Iran su ke yi, da gwale jaruntar da su ka nuna. Amma Yan izala masu hankali da imani duk sun yabawa kokarin amma wasu saboda cutar bangaranci da ta rufe idanuwansu yadda basa iya kallon koyarwar musulunci, Annabi da sahabbansa, haushi su ke ji da sukar Iran. Duk wanda ke jin haka ya caji imaninsa, saboda ya kaucewa tarbiyar musulunci. Annabi ya yi yarjejeniyar sadaukar da rayukan musulmi don kare Ahlul Kitabi a Madina matukar sun cika sharuddan yarjejeniya. Wannan shine koyarwa Allah da Annabinsa.

Matukar muka ci gaba da rura wutar bangaranci, haka nan musulmi zamu ci gaba da samun kalubale irin na Gaza amma mu kasa katabus. Mutane biliyan biyu, da kusan rabin fadin kasar duniya da arzikinta amma mun kasa katabus, wasu sun yunkura kuma muna dakile su maimakon karfafa su. Allah ka raba mu da ci gaba da zama taron tsintsiya ba shara.

Ali Abubakar Sadiq

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories