Majalisa Ta Sahalewa Tinubu Ya Ranto $500m Daga Bankin Duniya

A jiya Laraba ne majalisar dattawa ta amince da buƙatar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu Na karɓo rancen dala miliyan 500 domin samar da mitocin wutar lantarki a kasar.

 An aminta karɓar kuɗin ne ga Hukumar Kamfanonin Gwamnati (BPE) bayan an yi nazarin rahoton kwamitin majalisar dattijai mai kula da basukan gida da waje wanda mataimakin shugaban kwamitin, Sanata Haruna Manu (Taraba ta tsakiya) ya gabatar.

Rancen kuɗin na daga cikin lamunin dala biliyan 7.94 na bankin duniya wanda shugaba Bola Tinubu ya nemi amincewar majalisar dattawa tun a ranar 1 ga Nuwamba, 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories