Shugaban makaranta ya tattara kudin dalibai na WAEC da NECO ya gudu kasar waje

Shugaban wata makaranta ta sakandire mai zaman kanta ya tattara kudaden jarrabawar WAEC da NECO da iyaye suka biyawa 'ya'yansu ya shilla zuwa kasar waje.

Wani shugaban wata makaranta mai zaman kanta dake garin Ibadan, Jihar Oyo, ya tattara kudin dalibansa na jarrabawar kammala karatun sakandire (SSCE) ya tsere zuwa kasar waje.

Iyayen yara ne ke biyawa ‘ya’yansu kudin jarrabawar WAEC da NECO a makarantu masu zamansu.

Shugaban makarantar ya karbe kudin iyayen yara sannan ya siyar da dukkan kadarorinsa, da suka hada da gidansa da yake zaune, ya shilla ya bar Najeriya.

Ministan Ilimi: Tahir Mamman

Jaridar Aminiya Hausa ce ta wallafa labarin wanda ta ce ya samo asali ne daga shafin wata mata mai suna Adejoke Lasisi.

Jaridar Tribune ta rawaito cewa shugaban makarantar mai suna Sunday Adeyemi ya sayar da har ita kanta makarantar tasa a sirrance kafin ya tsere.

DUBA WANNAN: Tinubu ya bawa tsohon shugaban INEC Farfesa Attahiru Jega mukami

Aminiya ta ce Adejoke ba ta bayyana sunan shugaban da sunan makarantar sa ba amma ta bayar da tabbacin cewa lamarin ya faru.

A cewar Tribune, Sunday ya shafe fiye da shekara 20 yana tafiyar da makarantar kafin faruwar wannan lamari.

A yanzu haka daliban shekarar karshe a makarantun sakandire suna rubuta jarrabawar WAEC sannan kuma ana yin rijistar jarrabawar NECO wacce za a fara a watan Yuni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories