Babu Abunda Tafiya Yajin Aiki Zai Ƙara Sai Matsi-Gwamnan Bauchi Ga NLC

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi kira ga ƙungiyoyin ƙwadago (NLC) da su dubi Allah su sake dubi ga yajin aikin da suke shirin faɗawa a ranar Litinin.

 Gwamnan ya yi wannan roƙo ne a ranar Asabar a wata ganawa da ya yi da gwamnonin jihar Abia, Alex Otti;  da Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki;  da kuma mambobin kwamitin ayyuka na jam’iyyar PDP na ƙasa.

 Gwamnan ya nuna matuƙar damuwarsa kan yadda tafiya yajin aikin zai iya ƙara da gurgunta tattalin arzikin ƙasar tare da janyo wa ma’aikata wahala.

Dama dai a ranar Juma’ar da ta gabata ne ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya da ta ƴan kasuwa suka sanar da tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani a ƙoƙarin su na nuna rashin amincewarsu da gazawar gwamnatin tarayya ta ƙara mafi ƙaranci albashi ya koma N60,000 sannan kuma a janye ƙarin da aka yiwa wutar lantarki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories