Ba Don Ni Ba Da Yanzu Babu Labarin Tinubu A Siyasa – Atiku

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar,ya fito yana iƙirarin cewar duk masu yi masa gani-gani su sani cewar Tinubu fa da Bazar sa ya taka rawa a siyasa.

 Atiku ya ƙara da cewa In ba don shi ba da tuni an hamɓarar da Tinubu tun yana gwamnan jihar Legas a farkon jamhuriya ta hudu.

 Sai dai kuma a ranar Alhamis, mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima,a ƙoƙarin sa na mayar da martani ya bayyana cewa da Atiku da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, dukan su babu wanda Tinubu bai taimaka ba a lokacin da duniya ta juya musu baya suke fuskantar tsangwama.

 Mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa sai da gidan Tinubu da ke Bourdillon, Ikoyi, Legas, ya zama mafaka ga Atiku a lokacin da jam’iyyar PDP ta yi masa atishawan tsaki.

”Shugaba Tinubu ya dade da zama bango kuma mafaka ga ƴan siyasa saboda a lokacin da Atiku Abubakar aka koreshi a jam’iyyar PDP, wurin Tinubu ya ruga ya je neman mafaka kuma ya samu har ya sami damar fitowa takarar shugabancin ƙasar nan,” cewar Shettima a yayin kaddamar da kayatacceb gidan mataimakin shugaban ƙasa A Abuja.

 A nasa ƙoƙarin mayar da martani ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, da ya fitar a ranar Lahadi, Atiku ya ce Shettima ”Shashi faɗi kawai ya ke yi,” inda ya kara da cewa “in akwai wanda ya mori wani to tabbas Tinubu ne ya mori Atiku.”

 Ya kuma ƙara da cewa ba dan shi ba da Tinubu Bai wanye lafia ba lokacin yana gwamnan Legas.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories