Hajji: Wata Hajiya daga Najeriya ta kashe kan ta a Madina

Hauwa'u Mohammed ta rasu, bayan abin da hukumomin ƙasar Saudiyya suka gudanar da bincike suka gano cewa ta kashe kanta ne, ta hanyar faɗowa, da gangan, daga saman benen masaukinta da ke Madina

Wasu maniyyata guda biyu ƴan asalin jihar Kwara da ke aiwatar da aikin Hajjin bana a ƙasar Saudiyya daga jihar Kwara; Salihu Mohammed da Hawawu Mohammed, sun rasu a birnin Madina.

Sakataren zartarwa na Hukumar Alhazai ta Jihar Kwara, AbdulSalam AbdulKabir, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

A cewar sa, yayin da Salihu Mohammed ya rasu a sashin kula da marasa lafiya na musamman na asibitin gwamnati da ke Madina bayan ya fara jinya cikin ƙanƙanin lokaci.

DUBA WANNAN: Kano: HISBAH ta kama mawaki saboda jan aya ba daidai ba a cikin waka

Hauwa’u Mohammed ta rasu, bayan abin da hukumomin ƙasar Saudiyya suka gudanar da bincike suka gano cewa ta kashe kanta ne, ta hanyar faɗowa, da gangan, daga saman benen masaukinta da ke Madina.

Hukumomin Saudiyya da na jihar Kwara sun bayyana faruwar lamarin a matsayin abin takaici gami da bakin ciki tare da mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories