Rashin Ɗa Namiji Ya Sa Wata Matashiya Gadon Sana’ar Wanzanci A Kano

Hassan Gambo matashiya Mai Sana’ar Wanzanci a wata zantawa da TRT Afirka ta yi da ita ta bayyana yadda ta tsinci kanta a wannan sana’a.

”Suna na Hassana Gambo wacce aka fi sani da ‘Wanzamiya’ a unguwar Dakata jihar Kano, ina yin Aski ,Shayi,Gyaran jariri,sannan kuma ina yin shayi na zamani wanda ake sa wando.

sana’a ta Wanzanci na gane ta ne gaba da baya kuma sannan na taso naga ana yi wanda mahaifina Alhaji Gambo Mai Askin ‘Barber’ ya koya min.”

”A yanzu haka mahaifina shine shugaban wanzamai na ƙaramar hukumar Nasarawa.Ni kuma a yanzu ni ce Shugabar mata wanzami ta ƙaramar hukumar Nasarawa.

Hassana ta bayyana cewa rashin samun Ɗa namiji da Ubangiji bai ba wa mahaifinta ba kuma yana da kyau ace a cikin gidansa akwai wanda ya gaje sa wannan shine babban ddalili da ya sa na tsunduma sana’ar aski.

Ta kara da cewa ta tsunduma sana’ar aski ne tun tana ƴar shekara goma”.A lokacin idan mahaifina yana yi sai ya kira ni inzo In zauna in gani tun nasiha zama har abin yazo ya shiga raina na fara zama ina ganin yadda ake yi,har na kai matsayin da mahaifina ya fara ba ni har hannu na ya faɗa.A yanzu haka in aka gayyace mu gidan suna mahaifina baya taɓa yaro ni yake barwa in yi.”

Harkar ƙaho kuwa ta ce tun ana yin irin na zamanin da ya ke koya mata , a lokacin tun tana yi tana kuka bata so saboda shi ƙaho aiki ne da idan baka saba ba bakin ka ciwo zai yi.Amma daga baya abin ya zamo mata jiki ta saba.

Hassana ta ce da kuɗin wannan sana’a take yiwa kanta komai,kama daga kan hidimar makaranta har zuwa rayuwar yau da kullum.Sannan kuma ta bayyana irin nasarori da kuma ƙalubale da take fuskantar duba da irin yankin da ta taso ana yawan ƙorafin cewa bai kamata ƴa mace ta rike sana’ar Wanzanci ba

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories