Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Sabon Ranar Bikin Dimokraɗiyya

Gwamnatin tarayya ta sake yiwa ranar bikin dimokuraɗiyya fasali inda ta ayyana ranar Laraba 12 ga watan Yuni a matsayin ranar hutu domin tunawa da ranar dimokraɗiyya.

 Aishatu Ndayako Babbar sakatariya a ma’aikatar harkokin cikin gida, ita ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a yau Talata.

Haka kuma an ji Olubunmi Tunji-Ojo, ministan harkokin cikin gida na Najeriya yana cewa ya kamata ƴan Najeriya su dage kan tsarin mulkin dimokuradiyya.

 “Yayin da muke bikin wannan rana ta dimokuraɗiyya , kar mu manta da irin ƙoƙarin da magabatan mu suka yi wajen ganin Ƙasa Najeriya ta cigaba da zama maɗauri ɗaya, samun kwanciyar hankali, zaman lafiya da rashin rabuwar kai” in ji Ministan.

Tunji-Ojo ya ƙara da cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ƙuduri aniyar kawo sauyi mai kyau domin farfado da tattalin arzikin kasa da inganta tsaro.

Sannan Ministan ya yi kira ga ƴan Najeriya da sauran abokan arziki da su yabawa irin ci gaban da aka samu zuwa yanzu tare da fatan samun kyakkyawar makoma ga dimokradiyyar Najeriya.

 In ba a Manta ba dai a watan Yunin 2018 ne tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya canza ranar dimokuraɗiyya inda aka ayyana ranar 12 ga watan Yuni a matsayin sabuwar ranar a Najeriya,Duk da kasancewar shekarun baya 29 ita ce ranar da ake wannan biki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories