Jerin Shugabannin Ƙasa Da Suka Yi Ƙarin Mafi Ƙanƙantar Albashi Daga 1954-2024 

Tattaunawa da ke cigaba da gudana tsakanin gwamnatin tarayya da ƙungiyar ƙwadago game da mafi karancin albashi wanda har yanzu dai ana ta jeka ka dawo

 An dai ji yadda Ƙungiyoyin Kwadago, ,Gwamnatin Tarayya (FG) da kamfanoni masu zaman kansu suke ta zama game da yajin aikin da suka shiga a fadin kasar wanda ya dakatar da muhimman ayyuka a kasar a makon da ya gabata

 Ƙwadago ta bukaci N494,000 yayin da FG ta ce N60,000 a matsayin mafi karancin albashi a Najeriya.

 A ci gaba da tattaunawa kan batun mafi karancin albashi, WikkiTimes, ta zaƙulo sunayen shugabannin Najeriya da suka yi ƙarin sabon mafi karancin albashi a lokacin da suke rike da madafun iko.tun daga 1954 zuwa yau.

Obafemi Awolowo

 Cif Obafemi Awolowo, Firimiyan wancan lokaci shi ne ya fara aiwatar da tsarin mafi ƙarancin albashi na farko a shekarar 1954. Wannan manufar ita ce mafarin ɓullar fara zaman tattaunawa game da mafi ƙarancin albashi a Najeriya bayan samun ƴancin kai.

 A cewar gidauniyar Awolowo, Marigayi Awolowo” ya bullo da nasarar kawo tsarinr mafi karancin albashi a Najeriya na farko inda aks biya mafi karancin albashi a shekarar 1954 wanda ya ninka adadin kudin da ake biyan ma’aikata masu irin wannan matakin a wasu sassan Najeriya.”

 Bayan Najeriya ta samu ƴancin kai a 1960, Awolowo ya ci gaba da bada himma tattaunawa kan mafi karancin albashi na kasa.  Ya mai da lamarin yakin neman zabe a matsayinsa na shugaban kungiyar Action Group.  A 1959, Awolowo, ya bayar da shawarar biyan mafi karancin albashi na fam biyar ga ma’aikatan tarayya sai dai ya sha kaye a zabe a hannun Sir Abubakar Tafawa Balewa.

 Shehu Shagari

 Shugaba Shehu Shagari wanda ya mulki Najeriya a jamhuriya ta biyu ya kafa dokar ƙarin albashi mafi karancin albashi a shekarar 1981. Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya na wancan lokacin Hassan Sunmonu ya kara matsa kaimi kafin daga bisani suka cimma matsaya da gwamnati kan biyan mafi karancin albashi na N125 duk wata. Adadin ya kai dalar Amurka 204 a wancan lokacin.

Abdussalami Abubakar

 Janar Abdussalami Abubakar ya karbi mulki a shekarar 1998 bayan rasuwar Janar Sani Abacha. A matsayinsa na shugaban rikon kwarya, ya Yi karin albashi zuwa N3,500 daga N450 a lokacin.  Inda kuma Daga baya ya mika mulki ga zababben shugaban kasa a shekarar 1999.

 Olusegun Obasanjo

 Lokacin da Obasanjo ya dawo a matsayin shugaban kasa, kungiyoyin farar hula da kungiyoyin ƙwadago suka sake kunno kai.  Bayan dakatar da su a lokacin mulkin soja.   Jim kadan bayan karin albashi da Abdussalami Abubakar ya yi, tsakanin 2000 zuwa 2001, Shugaba Obasanjo a wa’adinsa na biyu ya ƙara mafi karancin albashi zuwa N5,500. Wannan ƙari shi ne ya daga darajar ma’aikata da dama a Najeriya, amma kuma hauhawar farashin kayayyaki ya yi karu inda aka dauki shekaru masu yawa kafin gwamnati ta iya shawo kan lamarin. A shekarar 2007 Mafi ƙarancin albashi ya kai N7,500 

Goodluck Jonathan

 A shekara ta 2010 lokacin gwamnatin shugaba Yar’adua/Jonathan ya daidaita mafi ƙarancin albashi zuwa 11,000 daga N7,500.  Biyo bayan bukatu da korafe-korafen da ma’aikata suka yi ta yi ta hannun kungiyoyinsu, a shekarar 2011, Shugaba Goodluck Jonathan ya sake kara mafi ƙarancin albashi zuwa N18,000.  Duk da dai a lokacin Kungiyar kwadago ta gabatar da kudirin Naira 52,000 inda daga baya kuma ta rage zuwa N22,000 kafin daga bisani aka cimma yarjejeniya da gwamnati zuwa N18,000.

 Muhammadu Buhari

 Shugaba Buhari ya ƙara mafi karancin albashi zuwa N30,000 a shekarar 2019 tare da sanya hannu kan sabuwar dokar mafi karancin albashi a waccan shekarar.  Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta koka kan karin albashi sakamakon rubanya farashin man fetur da sauran batutuwan da suka shafi hauhawar farashin kayayyaki.  NLC dai ta gabatar da N56,000 daga N18,000 na wancan lokacin amma bayan tattaunawar da bangarori uku ta yi sai aka ƙaddamar da N30,000 ya zama sabon mafi ƙarancin albashi na kasa.  N30,000 ne mafi ƙarancin albashi da aka yi ta biya har zuwa  watan Afrilun 2024. Inda NLC ta dage kan cewa dole ne sabon mafi karancin albashin ya fara aiki daga ranar 31 ga watan Mayun 2024, amma hakan ya faskara.

Bola Tinubu

 Don rage tasirin raɗaɗin cire tallafin man fetur da kuma walwala a Najeriya, Shugaba Tinubu ya yi wa ma’aikata alkawarin biyan albashi a shekarar 2024 wanda zai nuna halin da tattalin arzikin kasar ke ciki a halin yanzu.  Bayan karewar dokar mafi karancin albashi da ake da ita, wacce za a sake duba ta duk bayan shekaru biyar, Tinubu ya kaddamar da shawarar biyan ma’aikatan gwamnatin tarayya albashin N35,000 a duk fadin kasar. Inda A watan Janairu, ya kaddamar da kwamitin bangarori uku, amma hakan ya kasa cimma matsaya kan mafi karancin albashin da kasar za ta amince da shi.

Sai dai Jihar Edo ta sanar da karin mafi karancin albashi zuwa N70,000 daga ranar 1 ga Mayu, 2024. Jihar Legas na biyan albashin N35,000 tun daga watan Janairun 2024.Sai takarar ta jihar Kano ita kuma tana biya ma’aikatan gwamnati N10,000 sau biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories