Ruɗewa Ya Sa Mutane Sun Kasa Gane Faduwar Da Na Yi ”Swagger Ce” – Tinubu

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya yi ƙarin haske game da tsautsayin da ya faru da shi  a dandalin Eagle Square, Abuja,a safiyar ranar Laraba,Da yake magana a wajen liyafar cin abinci da aka shirya, shugaban ya ce faduwar da ya yi “Swagger ce”, Kafofin sada zumunta su basu gane hakan ba suke ta yamaɗiɗi.

“A safiyar yau, na yi swagger ya kuma watsu a dukkan kafofin watsa labaru. Ƴan soshiyal mediya sun rude ba su gane cewar faɗuwar da na yi rawar ‘buga da Babbar riga nake yi ba ”.

Shugaban ya ƙara da cewa ranar bikin Dimokuradiyya ai dole a yi rawa a cashe a matsayin sa na cikakken bayarbe shi ya sa ya yi rawar ‘dobale’.

Sai dai kuma al’ummar kasar ta ɓangarori daban daban sun fito sun bayyana ra’ayoyin su game da faɗuwar inda wasu suke alhini wasu kuwa gani suke alhakin kunci rayuwa da talaka ke ciki ne ya fara tasiri.

Ga kaɗan daga cikin ra’ayoyin:

iklima Usman ”Ta ce Haba gaskia ƴan Najeriya bakuda kirki shugaba ku ya faɗi kudinga jin ɗaɗi.”

Confidence ta ce :”Ai Ni wallahi daɗi naji”

Muhammad Isa ” ya ce wallahi Abun tausayi mutumin nan na tausaya masa”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories