Babbar Sallah: An Sace Ragon Liman Na Layya A Jos

Malam Imam Abdulkadir, babban limamin Masallacin Al’ummar Ali da ke yankin karamar hukumar Bassa a Jihar Filato, ya gamu da sharrin barayin Rago.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa wasu barayi sun bi dare, yayin da ake tsaka da ruwan sama kamar da bakin kwarya, sun sace ragon layyar Malam Abdulkadir washegarin Sallah.

Malam Haruna Yaqub, Limamin Wani Masallaci a yankin, shine ya sanar da hakan jim kadan bayan idar da Sallar Idi yayin da ya ke gabatar da huduba. Ya bayyana barayin a matsayin cikakkun marasa tausayi da tsoron Allah.

“An bi dare an sace ragon layya da Limamin mu ya siyo. Lamarin ya matukar girgiza mu kuma mun yi matukar mamakin samun wannan labari.

DUBA WANNAN: Jos: An kama wani matashi daure da jigidar bama-bamai a harabar banki

“Hakan ya tabbatar mana lallai cewa wadannan barayi basa tsoron Allah. Abin tsoro ne a ce rashin imanin mutane har ya kai ga satar ragon layya da aka siya domin hidimtawa addini,” a cewar Malam Yaqub.

A karshe, Malamin ya yi kira ga jama’a da su ji tsoron Allah tare da tuba da kuma daina aikata duk wani abu da ya ke haramun ne a addinin Musulunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories