Abinda Atiku Da Buhari Suka Tattauna Yayin Ganawarsu A Daura

Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya kai wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara a mahaifarsa, da ke Daura a jihar Katsina a ranar Asabar, 22 ga watan Yuni.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya isa filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua dake Katsina da misalin karfe 11:25 na safe inda daga nan ya wuce Daura kai tsaye inda ya samu ganawa da Buhari.

Da yake zantawa da manema labarai a Katsina, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce ya kai ziyarar ne domin taya tsohon shugaban kasar murnar kammala bikin babbar Sallah lafiya.

NIGERIAN TRACKER ta rawaito cewa Atiku ya sanar da Buhari burinsa na yin hadaka da wasu jam’iyyu domin tunkarar zaben shugaban kasa na shekarar 2027, kamar yadda wani magoyin bayan Atiku, Abdul-Aziz Na’ibi Abubakar, ya wallafa a shafinsa na ‘X’ @jrnaib2.

KARANTA: Abinda Ribadu da Abbba suka tattauna yayin ganawarsu

A cewar majiyar Nigerian Tracker, Buhari ya bawa Atiku kwarin gwuiwar ya mayar da hankali wajen tattaunawa da jam’iyyun adawa domin yin hadaka tare da bayyana cewa hakan yana kara karfafa dimokradiyya.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa irin wannan hadaka ta jam’iyun adawa ita ta bawa jam’iyyar APC damar kwace mulki daga hannu PDP a shekarar 2015.

Kafin ya bar Daura, Atiku ya jinjinawa tsohon shugaban kasa Buhari bisa rawar da yake cigaba da takawa na matsayin dattijon kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories