Yana Da Kyau Mu San Darajar Kujerar Sarkin Musulmi – Shettima Ga Gwamnan Sokoto

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya shaidawa gwamnatin jihar Sokoto cewa mai martaba Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III sarki ne da dole a yi kishin sa kuma a kare martabar sa.

 Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a wurin taron zaman lafiya da tsaro na yankin Arewa maso Yamma, da ake gudanarwa yanzu haka a jihar Katsina wanda ake watsawa kai tsaye daga gidan talabijin na Trust.

“A dukkan al’amruan ƙasar nan, mai martaba Sarkin Musulmi, ina so in yi amfani da shi a matsayin misali da shi da dukkan sarakunan da ke wurin nan.”

“Kuma ina so in aika saƙo ga mataimakin gwamnan Sakkwato, ina so ka sani cewa tabbas, Sultan Sarkin Musulmi ne, amma girman sa ya wuce haka;  yana wakiltar wani babban jigo ne, da dukkan mu a ƙasar nan saboda haka muna bukatar mu yi kishin sa kuma mu basu kariya tare da nuna kishin kasa, ingantawa, don ciagaban al’ummarmu,” cewar Shettima.

 In ba Manta ba dai a yau ne Babban Daraktan kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC), Farfesa Isiaq Akintola, ya fito ya koka kan cewar sun sami rahoton cewa gwamnatin Sokoto na shirin tsige Sarkin Musulmi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories