An Buƙaci Tinubu Ya Tsawatar Kan Cin Zarafin Ƴan Jarida

Cibiyar ci gaban jama’a da masu zaman kansu (PPDC) ta buƙaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya gargadi jami’an tsaro game da kame da kuma tsoratar da ƴan jarida da suke yi.

 Cibiyar ta bayyana barazana da kame da masu aikin jarida ke fuskanta a yayin gudanar da ayyukansu sam baza su laminta ba kuma haka ba daidai ba ne.

Babban jami’in PPDC, Jubril Shittu, Shi ne wanda ya yi wannan kiran a Abuja a lokacin taron manema labarai, inda ya yi kira da a soke ko kuma a yi gyara ga dokokin da suka tauye ƴancin ƴan jarida, kamar dokar ta’addancin Intanet.

 Shittu, wanda ya samu wakilcin Lucy James Abagi, Darakta mai kula da hadin gwiwa da kirkire-kirkire na cibiyar, ya bukaci gwamnati da ta daina amfani da dokar laifuka ta yanar gizo wajen murƙushe kafafen yada labarai da ma sauran ayyukan soshiyal mediya.

“Kame da cin zarafi suna matuƙar barazana ga ƴancin ƴan jarida da kuma zagon kasa ga dimokuradiyyar mu. A cikin shekara nan 2024, abokan aikinmu na Cibiyar Innovation da Ci gaban Jarida (CJID) sun tattara kamen ƴan jaridu fiye da mutane 34 a ƙasar nan.

“Saboda haka Muna kira ga gwamnatin Najeriya da ta ba wa ƴan jaridu hakkin su tare , da tabbatar da kariyarsu, sannan kuma a samar da dokar da zata baiwa ƴan jaridu da kafafen yada labarai damar samun  ‘yanci ba tare da tsoro ba,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories