Duk Da Haramcin Cin Hanci,Sanata Oyewumi Ya Labarta Yadda Ya Sayi Ƙuri’u

Dubban Ƴan Najeriya sun yi tir da irin iƙirarin da Sanata Olalere Oyewumi, dan majalisar dattawa na jam’iyyar PDP ya yi, inda ya bayyana yadda ya sayi ƙuri’u a zaɓen da ya gudana a shekarar 2023.

 Tun dama dai an sani cewar Siyan kuri’u na ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da suka dabaibaye hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) a yayin gudanar zaɓe.

A cikin wani faifan bidiyo da ya bayyana an ji Oyewunmi, wanda shi ne mataimakin shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa, ya na mai bayyana yadda ya aiki mutanen sa a ranar jajibarin zaɓe da kuɗade don su siya kuri’u amma sai aka sami al’adu magoya bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) suka ƙi amincewa da wannan buƙata.

A jawabin na sa wanda ya yi da Yaren yarbsnci, shugaban, wanda ke wakiltar gundumar Osun ta Yamma, ya cigaba cewa“Na gwada duk dabarar da na sani don ganin na ci rumfar gidan Onilu (Ile Onilu) amma abin yaci tura.

 “Bayan na gama kashe kuɗi haka na sake ɗiban kuɗina na baiwa Ten Ten don ya rabawa mutane don mu samu mu sayi kuri’u.

 “Hakan ya sa na tuntubi wadannan mutane saboda ba bu yadda za a yi inci Sanata In ban samu haɗin kansu ba.  Ni ne na yi waya da Ayandosu daga Abuja na neme shi da ya dawo PDP.  Na ce masa yana da hazaka kuma jam’iyyar da yake yi wa hidima APC ba za ta bari ya zama wani abu ba.”

Da yake mayar da martani kan lamarin, shugabancin jam’iyyar ta APC ta bakin shugabanta, Tajudeen Lawal, ya ce ikirari Sanata Oyewunmi ya nuna cewa zaben Osun ba a Yi gaskia ba.Haka ma ƴan Najeriya da dama sun fito sun tofa albarkacin bakin su inda wasu ke cewa inda ace Najeriya ana adalci da ”sai mu zuba ido muga irin hukuncin da za a yi masa”.

Wasu kuwa cewa suka yi ”Ina hukumar EFCC”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories