Mijin Tsohuwar Minista Dizani Ya Nemi Da Ta Daina Amfani Da Sunansa

Rear Admiral Alison Amaechina Madueke ya nemi kotu da ta hana tsohuwar matarsa, Diezani Alison-Madueke yin amfani da sunansa Alison Madueke saboda yanzu babu aure tsakanin su.

 Ya roki kotu da ta umurci Diezani ta koma amfani da tsohon sunan ta na da ‘Agama’ ta kuma siya shafi a jaridu domin a wallafa sabon sunan na ta a jaridun kasashe biyu na Najeriya da Ingila kan sanarwar daina amfani da wancan sunan.

 Shi dai wannan ƙara An shigar da shi ne a wata babbar kotun Legas mai lamba LD/15144HD/2024, Inda ta buƙaci tsohuwar minista ta daina amfani da sunan wanda ya shigar da karar, wanda hakan na da matukar tasiri ga shari’a da kuma kalubale ga mai karar saboda wacce ake ƙarar yanzu haka tana fuskantar shari’a a ƙasa Najeriya da Birtaniya.

Takardar ƙarar ta bayyana cewa,Diezani da mijinta sun rabu tun a watan Mayun 2015 bayan an bata minista, kuma a watan Nuwamba 2021, bisa dalilin rabuwae auren sai, Diezani ta shigar da kara kan a raba auren (Kati NSD/MG345/2021) a Babbar Kotun Nassarawa. Sashen Shari’a na Jihar Nassarawa, wanda ke zaune a Mararaba Gurku kuma a ranar 13 ga Afrilu, 2022, an zartar da hukunci a cikin Suit No. NSD/MG345/2021 ta Hon.  Justice A.A.  Ozegya, wanda shi ne ya raba auren.

 Sakamon rabuwar sai Alison Madueke Ya shigar da ƙara inda yake umurtar lauyoyinsa da su rubuta wasika zuwa ga Diezani akan ta daina cigaba da amfani da sunan sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories