Hukumar NSCDC Ta Rufe Kamfanoni Masu Zaman Kansu A Abuja

Rundunar tsaron farin kaya ta NSCDC, ta garkame wasu kamfanonin gadi su uku masu zaman kansu a Abuja.

Kwamanda rundunar da ke babban birnin tarayya, Olusola Odumosu shi ne ya jagoranci aikin rufe kamfanonin tare da sa ido a ranar Laraba domin tabbatar da tsaro a garin.

Kamfaonin da aka rufe su ne Ochacho Security Nigeria Ltd a Idu Industrial layout, Justigo Security and Allied Services a Gwarimpa da Macro Security Consult and Service a Wuse 2, Abuja.

“Mun tura musu gayyata sun ki halarta don haka ba mu da wani zabin daya wuce mu rufe domin su daina gudanar da ayyukan da suke yi ba bisa ka’ida ba kuma mun tilasta musu yin rajistar da ya dace,” in ji shi.

Kwamandan ya ce, a daya bangaren kuma, kamfanin tsaro na Justigo, an kulle shi ne saboda gudanar da aiki da kakin kafa guda biyu.

“Sannan kuma an tuhume ku da laifin yin barazana ga jami’an tsaron kasa, kin amincewa ku karbi lasisi, aikin gadi ba tare da izinin ba.

“Babu wani nuni na lasisin aiki kuma ba ku sabunta lasisin ku ba a cikin shekaru biyu da suka gabata ba kuma idan kuna musu cewa kuna da, babu wata shaida da za a nuna,” in ji shi.

Mista Odumosu ya kara da cewa, an rufe kamfanin Maco ne saboda ba a yi wa kamfanin rajista ba kuma sun shafe shekaru suna aiki ba bisa ka’ida ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories