Gwamnan Kogi Ya Tsallake Rijiya Da Baya Yayin Da ‘Yan Bindiga Cikin Kakin Soja Suka Bude Wa Ayarinsa Wuta

Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya tsallake rijiya da baya inda wasu ‘yan bindiga cikin kayan sojoji suka kai masa jerin hari har guda uku a kan hayarsa daga Lokoja zuwa Abuja.

Sai dai gwamnatin jihar, ta ce, dukkanin wannan yunkuri ne kawai na janyo tashin-tashina gabanin babban zaben gwamnan jihar da za a yi ranar 11 ga watan Nuwamban da ke tafe.

A cewar wata sanarwar manema labarai mai kanun cewa yunkurin kashe gwamna da ke dauke da sanya hannun kwamishinan yada labarai da sadarwa, Kingsley Femi Fanwo, ta ce, masu kai harin wa tawagar gwamnan da suke sanye da kakin sojoji sun bude wuta ga motocin ayarin gwamnan ciki har da motar da gwamnan ke ciki.

Femi ya ce sau uku a wurare daban-daban ana kai wa gwamna Bello hari a kan babban hanyar Lokoja zuwa Abuja da kuma wanda aka kai masa na karshe a yankin Kwali da ke cikin birnin tarayya wajajen karfe 4.20pm na yammacin ranar Lahadi.

Fanwo ya kara da cewa cikin hanzari jami’an tsaron da suke rakiya wa gwamnan suka fuskanci maharan tare da dakile aniyarsu na hallaka gwamnan.

“Gwamnatin jihar Kogi na shelanta wa duniya cewa an yi yunkurin kashe gwamnan jihar, Alhaji Yahaya Bello, CON, ‘yan mita kalilan da cikin Abuja, a lokacin da ke kan hanyarsa ta zuwa wani aikin hidimta wa jama’a daga Lokoja.

“Harin ya faru ne wajajen karfe 4 na yammacin ranar Lahadi 22 ga watan Oktoban 2023.

“Maharan wadanda suke sanye da kayan sojoji sun tunkari ayarin gwamnan tare da fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi a jikin motocin da ke tawagar ciki har da na gwamnan. Nan da nan jami’an tsaron gwamnan suka dakile shirin shaidanun da ba a san ko su waye ba da suka yi amfani da kayan sojoji.

“Sau uku ke nan ana kai wa gwamnan harin a wurare daban-daban, na karshe wanda aka masa shi ne a kusa da Kwalli da ke birnin tarayya Abuja wajajen karfe 4.20pm.”

Daga nan sanarwar ta nemi hukumomin tsaro da su gaggauta kaddamar da bincike kan lamarin domin gano wadanda suke kai wa gwamnan harin domin kare faruwar hakan a nan gaba.

Sanarwar ta yi zargin cewa, masu neman janyo fitina da tashin hankali gaban zaben gwamnan jihar da zai gudana a ranar 11 ga Nuwamba ne suke yunkurin haifar da tashin hankali domin kawo yamutsu a zaben.

“Muna kira ga al’umma da su ci gaba da kasancewa a ankare kuma su kai rahoton dukkanin wani motsin da suke zargi ga jami’an tsaro domin gaggawan daukan mataki. Gwamnati tana sane da nauyin da ke kanta na kare rayuka da dukiyar al’umman jihar,” kwamishinan ya shaida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories