Da dumi-dumi: Kotun koli ta yi fatali da bukatar Atiku kan sake bayyana shedar jabu akan Tinubu

 A yau Alhamis ne rahotanni suka bayyana cewar kotun Koli ta yi watsi da bukatar dan takarar Shugaban kasa Atiku Abubakar kan bukatar sa na neman sake bayyanar da sabbin shedar jabu akan Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

 Atiku ya bukaci kotu da ta bashi damar bayyanar da cikakken shaidu da aka samu daga bayanan takardun Tinubu a Jami’ar Jihar Chicago.

 Atiku ya bayyana cewa Tinubu takardun jabu ya mikawa hukumar zabe ta kasa (INEC).

 Sai dai Tinubu ya nuna rashin amincewarsa inda ya bayyana cewa bukatar Atiku ya wuce wa’adin kwanaki 180 da aka kayyade.

 A hukuncin da ya yanke a ranar Alhamis, mai shari’a Inyang Okoro, shugaban kwamitin mutane 7, yace kwanakin da aka diba don sauraron kararrakin zabe sun kare saboda haka babu kari babu ragi .

 “Ya kamata a lura da cewa kwanaki 180 da aka kayyade ba za a iya canzawa ba kuma ba za a iya tsawaita su ba … Korafe-korafen zabe kwanakin su a kayyade ya ke ne kuma suna da nasu tsarin .

Saboda haka Kotun ba ta da hurumin tantance duk wani batu da ya shafi ƙarar bayan kwanaki 180 wanda wanan kwanaki sun ƙare tun a watan Satumb 17. Wannan kotu ba za ta yi abin da ƙaramar kotu ba ta yarda da shi a sashe na 285 na kundin tsarin mulkin ƙasar ba.

 “Babu wani sabon gyara da za a iya gabatar wa akan hujjojin da ba su kunshe a cikin karar zaben kamar yadda aka bayyana a sashe na 132(7) na dokar zabe.  In akayi haka an karya dokar zabe

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories