Sanadiyyar Diban Ruwa A Rijiya Yaro Dan Shekara 7 Ya Rasa Ransa

An tsinci gawar Abdul-Hayi mai shekaru bakwai , a rijiya a jihar Kwara.

Yaron wanda ya fito da ga gidan Yaa-Lateef da ke titin Tinu, Akerebiata, a karamar hukumar Ilorin ta Gabas, rahotanni sun bayyana cewa ya fada cikin rijiyar ne yana tsaka da dibn ruwa in da tsautsayi ya ja kafarsa daya ya zame a cikin rijiyar da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Litinin.

Shugaban sashen yada labarai na hukumar kashe gobara ta jihar Kwara Hassan Hakeem Adekunle shi ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Talata.

 Ya ce wani Mista Idowu mazaunin unguwar shi ne ya sanar da ‘yan kwana-kwana ta wayar tarho .

A cewarsa, ‘yan kwana-kwana sun samu nasarar ciro gawar daga cikin rijiyar, inda daga bisani suka mika gawar ga dan uwan mamacin Malam Yussuf.

 Ya kara da cewa daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Prince Falade John Olumuyiwa ya nuna alhininsa ga me da faruwar lamarin.

“Ya bukaci jama’a da su kara taka tsantsan ga me da al’amuran yau da kullum  Olumuyiwa ya kuma umarce su da su daina tura yara masu karancin shekaru debo ruwa a cikin rijiya,” 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories