Yankin Da ‘Yan Bindiga ke Hana Ayyukan Noma A Garin Kaduna

Manoma daga yankin Kidandan da kuma Galadima na jihar Kaduna suna biyan haraji ga ‘yan fashi wanda hakan ke kawo cikas ga zaman lafiya a tsakanin al’ummar wannan yanki. Manoman suna biyan harajin ne kafin su iya samun damar yin aiki a gonakinsu, yayin da sukuma wadanda suka fito daga kauyukan Angular Fala’u da Kerawa ake sace su a yayin da suke gudanar da ayyukan su a gonakin su.

 Malam Jamil Kidandan wani mazaunin kauyen Kidandan ya bayyana cewa, mutanen da ke zaune a yankunan galibi manoma ne, saboda haka suna biyan kudin da ya kai kimanin Naira 70,000 zuwa 100,000 kafin su sami damar gudanar da ayyuka a gonakin su ,Daily Trust ta ruwaito cewa duk manoman da suka yi tirjiya wurin biyan haraji sukan fuskanci barazana ko ko a sace su ko kuma wasu a kashe su ko kuma ma a kwace amfanin gonan su.

A cewar sa , ‘yan bindigan suna zama ne a gefen gari inda duk wani manoni da ya tunkaro su zai fara samu a yi ciniki kafin ya sami damar yin aiki a gonaki.

 Manomin ya kuma roki gwamnatin tarayya da jami’an tsaro da su kara kaimi a sansanonin ‘yan bindiga da ke kusa da karamar hukumar Giwa.

 Wani dan kauyen dake yankin wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya lissafo sunayen ‘yan bindigan da ke addabar mazauna yankin wadanda suka hada da Buhari, da mataimakinsa, Gana’i, yayin da cikon na ukun su kuma ana kiran sa Kwalameri.

Shi kuma Malam Jafar Anaba, wani shugaban wani kauye wanda harin ‘yan bindiga ya koro su daga kauyen su da ke Anguwar Salahu kusa da kauyen Kerawa, ya yi gargadin cewa za a iya samun karancin abinci a jihar idan har ba a dauki matakan da suka dace ba,kuma ya kara da cewa manoma da dama sun yi watsi da gonakinsu saboda yawan ta’adin da ‘yan bindiga suka yi a wurin.

 A halin da ake ciki, WikkiTimes ta yi kokarin tuntubar ASP Mansir Hassan, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar amma hakan bai samu ba, kuma har wayau bai ansa sakon tes da aka tura masa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories