‘Yan Bindiga Sun Bada Wa’adin Kwanaki 7 Ga Iyalan Mutanen da Suka Sace

‘Yan bindiga sun bayar da wa’adin kwanaki bakwai ga iyalan mutane 19 da suka yi garkuwa da su, inda su ka umurce su tara kudin fansa kimanin Naira miliyan 10 da buhunan shinkafa uku ko kuma su rasa ‘yan uwansu.

 City & Crime ta ruwaito cewa makwanni uku da suka gabata ne aka sami labarin ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen Kudiri da ke karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna inda suka yi garkuwa da mutane 23, amma sai dai hudu daga cikinsu sun yi nasarar tserewa a makon da ya gabata.

Wani dan uwan daya daga cikin wadanda abin ya shafa, mai suna Abdullahi, wanda ya zanta da wakilin Daily Trust a ranar Litinin, ya ce shugaban ‘yan bindigar ya kira su ta wayar tarho a ranar Asabar tare da yin barazanar kashe sauran mutanen 19 da suka rage in har bayan kwanaki bakwai ba a basu abinda suka bukata ba.

 Ya ce, “Ko da yake da farko shugaban ‘yan fashin ya nemi N20m , bayan tattaunawa, ya sauko da kudin fansa a ranar Asabar da misalin karfe 11 na safe.”

Ya kara da cewa, “Wasu daga cikin ‘yan uwan wadanda aka sace sun fara sayar da kadarorin su da suka hada da amfanin gona domin samun kudin fansar.

 Kawo yanzu dai babu wani martani daga kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Kaduna kan wannan batu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories