Dalilan Da Suka Sanya Gwamnatin Tarayya  Sakin Fursunoni Sama Da 4000  

Gwamnatin tarayya ta saki akalla fursunoni 4068 a dukkan cibiyoyin da ake tsare da su a fadin kasar nan a kokarinta na rage cunkoso a gidajen yari a kasar.

 Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, yayin da yake ba da sanarwar biyan tara da kuma diyya ga fursunonin da suka kasa biyan tarar da aka yanke musu, a jiya Asabar a Cibiyar Kula da Matsakaitan laifuka da ke Kuje, garin Abuja. Ya ce wannan karamcin ya yi daidai da ajandar sabunta cikar buri na Shugaba Bola Tinubu.

 “A ranar 17 ga Nuwamba, 2023, an sami kimanin fursunoni 80,804 a cikin gidajen gyaran hali guda 253 dake fadin ƙasar nan, wadanda adadin kayan bukatar su ya kai kasa da 50,000.  

Wannan ya nuna cewa gidajen gyaran hali sun yi cinkoso da yawa. Wanda ya zama dole mu fara wannan shiri na rage su ,  don magance cunkoson da ake fama da shi a Cibiyoyin gyaran hali.

 “A yau, mun ba da umarnin sakin aƙalla fursunonin 4,068 da ke zaman gidan yari daban-daban ba tare da karɓar tara ko diyya a hannun su ba, Yawancin fursunonin da ke tsare talakawa ne da ba za su iya biyan tarar da aka yanke musu ba.”

 “An yi nasarar tara kimanin N585,000,000.00 daga hannu masu hannu da shuni, kungiyoyi wanda suka tara a matsayin wani ɓangare na sauke alhakin zamantakewa.

 “Saboda haka, duk wani fursuna da ke gidan kurkukun wanda tarar sa bai wuce N1,000,000 za su amfani da wannan alfarma.  Bugu da ƙari, kuma zamu baiwa  kowannen su alawus din da zai ba shi damar komawa gida,” cewar ministan.

 Ministan ya kuma ƙara da cewa an bai wa fursunonin horon da ya kamata da nufin tallafawa rayuwarsu da kuma ba su ilimi don su sami abin dogaro da kai bayan an sallame su.

 Ya yi kira ga sauran al’umma da su karbi ‘yan kasar da suka dawo da hannu bibbiyu, inda ya bukace su da su guji nuna musu kyama domin hakan zai iya mayar da fursunonin da aka sako zuwa ga aikata laifuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories