Dalilan Da Suka Sa Ake Ganin Auren Bazawara Ya Fi Na Budurwa

Bazawara dai ita ce matar auren da suka rabu da mijinta sandin mutuwa ko kuma rabuwa.

Budurwa kuma ita ce wacce ba ta taba yin aure ba.

Mafi yawan samari ba su son auren bazawara, amma masana sun yi nuni da cewa, akwai fa’idoji da dama a cikin aurenta.

Ga dalilan masana kamar haka;

1. Za ka samu ladan sunna idan ka yi, domin ka yi koyi da Fyayyen Halitta SAW.

2. Auren macen da ta fi ka shekaru, akwai yiyuwar samun ingantacciyar rayuwar aure matukar akwai soyayya.

3. Hakika bazawara ta fi budurwa sanin makaman aiki a zamantakewar aure musamman ma idan ta samu saurayi wato wanda ta girma.

4. Bazawara tana hakurin zamantakewa fiye da budurwa domin ita budurwa ta kware wajen yaudara.

5. Bazawara ko wadda ta fi ka shekaru ta san halayen iyayen miji da yadda ake zama da su sabanin budurwa.

Shiga WhatsApp Channel ɗin mu don samu labarai 👇https://whatsapp.com/channel/0029Va4UqoPHrDZlMmAnVE3N

Daga Hajiya Mariya Azare

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories