Tsohon Shugaban Ƙasa Obasanjo Ya Caccaki Hukuncin Kotu Kan Zabe

Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya caccaki hukuncin da alkalan Najeriya suka yanke kan rikice -rikicen zabe, yana mai cewa bai kamata ace alƙalai uku zuwa biyar kawai su soke hukuncin zaɓen da miliyoyin mutane suka kaɗa kuri’a ba .

 Obasanjo ya bayyana cewar ikon da wasu ƙalilan daga cikin alƙalai suka yi abu ne da “ba za a amince da shi ba kwata-kwata.”

Tsohon shugaban kasar ya yi magana ne dangane da hukuncin da kotun daukaka kara ke ci gaba da yankewa kan takaddamar zaɓen 2023 da aka yi.

 In Dai ba a manta ba a makon da ya gabata ne dai wasu alkalan kotun daukaka kara suka yanke hukuncin zaɓe inda suka kori wasu gwamnoni uku .Gwamnonin sun haɗa da Abba Kabir daga Kano,Alwala Dauda na Zamfara Sai kuma Caleb Muftawang Na Jihar Filato.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories