Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Janye Tsige Gwamnan Jihar Nasarawa

Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta soke tsige gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa.

Bayan kammala zaɓe Hukumar INEC ta bayyana Gwamna Abdullahi Sule na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen watan Maris, amma kuma sai David Ombugadu na jam’iyyar PDP ya garzaya kotu akan bai yadda ba.

A cewar INEC, Sule ya samu kuri’u 347,209 inda ya doke abokin hamayyarsa wanda ya samu kuri’u 283,016.

Sai dai a hukuncin da aka yanke a ranar 2 ga watan Oktoba, kotun ta soke zaɓen Sule tare da ayyana Ombugadu a matsayin wanda ya yi nasara.

 Amma Sule, ta bakin lauyansa, Wole Olanipekun (SAN), ya roki kotun daukaka kara da ta soke hukuncin da kotun ta yanke, sannan kuma ya ɗaukaka kara.

Lauya Olanipekun ya kara da cewa kotun ta ki amincewa da gabatar da shaidun da suka gabatar a lokacin zaman kotun, inda ya kara da cewa an kawo BVAS a gaban kotun ne kawai ba tare da an dauke su a matsayin shaida ba.

Sai dai kuma a ranar Alhamis kwamitin alkalai mai zaman mutane uku suka gudanar da gagarumin taron cewa kotun sauraren kararrakin zabe ta jihar Nasarawa ta yi kuskure wajen yanke hukuncin cewa Sule bai samu rinjayen kuri’un da aka kaɗa a zaben ba.

Bayan nan kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da hukuncin da kotun ta yanke tare da tabbatar da sake zaben Sule a matsayin Halastaccen gwamnan jihar Nasarawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories