Taraba: Ɗan Takarar Gwamna Na NNPP Ya Ƙi Amincewa Da Hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara

Farfesa Sani Yahaya na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a jihar Taraba ya ƙi amincewa da hukuncin da kotun ɗaukaka kara da ke Abuja ta yanke a kwanakin baya inda ta yi watsi da karar da ya shigar kan Gwamna Kefas Agbu.

Anji cewar Kotun ɗaukaka ƙara ta amince da hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zabe wanda Ɗan takara gwamnan jihar Taraba ya shigar inda aka yanke hukunci  kan karar da ya shigar na ƙalubalantar zaben Agbu.

 Da yake mayar da martani kan hukuncin Ɗan takarar a jiya ya bayyana cewa, bai yadda da hukuncin ba saboda haka zai garzaya kotun ƙoli domin neman hakkinsa da na al’ummar jihar .

Yahaya ya ce sam babu adalci a hukuncin da kotun koli da kotun ɗaukaka ƙara suka yanke, na watsi da ƙarar sa, inda ya kara da cewa “hukuncin da kotunan biyu suka yanke sam babu adalci .”

Ya ce lauyoyi ne suka binciki takardun shari’ar da jam’iyyun suka shigar a kotun sauraron kararrakin zabe, kuma lauyan kotun shi ne ya gabatar da takardun a kotun amma sai dai ya bayyana yadda ya yi matukar mamakin ganin babu kusan shafuka takwas a jikin kwafin sun bata.

 Farfesa Sani Yahaya ya bayyana cewa shi da lauyoyin sa sun yi matuƙar kaɗuwa yadda kotu ta yi watsi da karar da ya shigar duk da ɓacewar shafuka takwas a jikin kwafin .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories