Tsamiya wasu Ƴaƴan itace ne da ke ɗauke da sinadirai masu gina jiki,Sinadarin sa ana iya samun antioxidant, anti-fungal, anti-bacterial, da anti-viral effects, da sauran fa’idoji.
Ana samun sa a yankin Afirka,Indiya, Pakistan, da sauran yankuna masu zafin yanayi.
Sinadaran dake jikin tsamiya
Magnesium: 26%
Potassium: 16% na DV
Iron: 19% na DV
Calcium: 7% na DV
Phosphorus: 11% na DV
Copper: 11% na DV
Bitamin B1 (thiamin): 43% na DV
Bitamin B2 (riboflavin): 14% na DV
Bitamin B3 (niacin): 15% na DV
Yana da alamomin adadin:
bitamin C
bitamin K
bitamin B6 (pyridoxine)
folate
bitamin B5 (pantothenic acid)
selenium
Ƴayan Tsamiya suna kama da ƴaƴan wake sai dai sun fi wake girma da kuma tsayi.
Ƴaƴan In suna ɗanye suna fitowa koraye ga su da tsami,Wani lokaci ana kiran su Dabinon” Indiya”.
Ƴaƴan Tsamiya suna da amfani ta fanni daban daban irin su girki,magani,da sauran amfani.
Girki
Ana amfani da tsamiya sosai wajen dafa abinci a ƙasashe irin su gabashin Asiya, Mexico, da kuma Gabas ta Tsakiya, da ƙasar Caribbean. Ganyen da ƴaƴan duka ana ci.
Ana miya, ana amfani da shi wurin gashi, ana haɗa abin sha, Tsamiya na ɗaya daga sinadaran miyar Worcestershire.
Amfanin Tsamiya Wajen Magani
Tsamiya na taka muhimmiyar rawa a wajen magance cututtuka a gargajiyance.
Ana amfani da tsamiya wajen magance cututtuka irin su
Gudawa
Kumburin Ciki
Zazzaɓi
Ciwon Daji
Ciwon zuciya
Har ila yau, anq amfani da ɓawon da kuma ganyen wajen magance rauni a jiki.