Ƴan Bindiga Sun Sace Kimanin Mutane 30 A Kaduna

Wasu ƴan bindiga sun sace wasu mutum 30 a kauyen Unguwar Liman da ke unguwar Gwada ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

 Mazauna yankin sun bayyana cewa waɗanda abin ya shafa sun haɗa da matan aure da yara ƴan kasa da shekara 2, kuma babu wanda yasan inda aka kaisu.

 Lamarin dai ya faru ne a ranar Lahadi da misalin karfe 11 na dare inda ƴan bindigar suka yi ta harbe-harbe tare da farwa al’ummar yankin.

Malam Jafar Anaba, wani mazaunin garin kuma basarake ya shaida wa Daily Trust a ranar Litinin cewa Ƙanin sa da wasu ƴan uwan sa na cikin waɗanda aka sace.

Ya ce kuma har yanzu ƴan bindigar ba su tuntuɓi iyalan waɗanda suka sace ba.

 “Ƴan bindigar sun shigo yankin tare da kwashe kimanin mutane 30,A cikin  waɗanda aka sace akwai ƴaƴana  da ƴan uwan ,” cewar malam kafar.

Ya ce mazauna garin sun yi kokarin neman agaji a daren da abin ya faru , amma babu hanyar sadarwa a wannan lokacin.

An yi ƙokarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Mansir Hassan,amma abin ya ci tura.

An ƙasa samun layin wayar sa kuma bai maida martani ga sakon kar ta kwana da aka aika masa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories