Gwamnan da ya buƙaci ƳarAdua ya sauka saboda rashin lafiya na fama da rashin lafiya

ƘaiƘayi Koma Kan Masheƙiya ,Baza kasan zafin abu ba sai ya sameka,furucin Olusegun Adeniyi Mai Baiwa tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Ƴar’adua shawara ga Rotimi Akeredolu.

Adeniyi ya yaɓa wannan magana ne sakamakon furucin da shi Rotimi yayi wa tsohon shugaban ƙasa Ƴar’adua game da tafiya jinya da yayi lokacin mulkin sa,Inda shima gwamnan a yanzu haka ya fice ƙasar don neman lafiyar sa a karo na biyu.

 A shekarar 2009,lokacin Rotimi yana a matsayin shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA),ya tada jijiyoyin wuya akan cewa sai dole tsohon shugaban kasa Ƴar’Adua ya yi murabus saboda fama da rashin lafiya da yayi a wancan lokacin wanda ya shafe watanni a kasar waje yana jinya.

 A wancan lokacin akwai zaman da aka yi na karrama shugaban kotun ɗaukaka kara  Mai shari’a Umar Abdullahi mai ritaya, a ranar 4 ga watan Disamba, 2009, inda Akeredolu ya tada zancen cewar Nijeriya fa na cikin tsaka mai wuya saboda gazawar Shugaba Ƴar’adua, ya kuma yi kira da babbar murya kan cewa dole Ƴar’adua yayi murabus saboda jinya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories